'Yan siyasan PDP ne suka sankame albashin sojoji a aljifansu, inji gwamnatin Buhari
- Idan ana maganar jin dadin sojojin Najeriya, PDP na da zarge-zarge da yawa da ke rataye wuyanta, inji gwamnatin Buhari
- Daya daga cikin ikirari dai shi ne cewa a tsawon shekaru 16 na shugabancin PDP, ‘yan siyasa ne suka sace albashin mafi yawan sojojin kasar nan
- A cewar fadar shugaban kasa, sojoji a lokacin sun mutu a fagen daga saboda rashin isassun harsashin da za su yaki 'yan ta'adda dasu
Aso Rock Villa, Abuja - Fadar shugaban kasa ta sake magana kan wasu daga gazawar da tsohuwar gwamnatin PDP ta yi a karkashin shugabanninta na tsawon shekaru.
A wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar, fadar ta yi zargin cewa a tsawon shekaru 16 da PDP ta yi tana mulkin kasar, sojojin Najeriya na cike da tsananin kunci.
An lamushe albashin sojoji
Sanarwar da jaridar Punch ta gani ta kara da cewa a lokacin albashin sojoji ya shiga aljihun 'yan siyasar PDP yayin da sojoji suke ta mutuwa a fagen fama saboda ba su da kayan aikin tunkarar 'yan ta'adda.
Babu taimakon soja daga kasashen waje
Har ila yau, sanarwar ta bayyana cewa a wancan lokacin, kasashe masu kawance da Najeriya na kasa da kasa sun ki baiwa kasar tallafin kayan aikin soji da agaji.
Fadar shugaban kasar ta ce:
“Ba za mu taba mantawa a zamanin PDP ba, al’ummar kasar nan na da sojojin bogi wadanda albashinsu ke shigewa aljifan ‘yan siyasar PDP yayin da sojojinmu jajirtattu suka mutu a yakin da suke yi da ‘yan ta’adda, sannan kawayenmu na duniya suka ki bai wa Najeriya kayayyakin agani da kayan aikin soja."
Manufar APC, kawo ci gaba
Shehu ya yi alfahari da cewa babban burin jam’iyyar APC shi ne gyara dimbin matsalolin da kura-kuran da jam’iyyar PDP ta haifar, musamman a fannin yaki da ta’addanci.
Yace:
“Ta'addanci na tsawon lokaci da barnar da jam’iyyar PDP ta yi a kan karagar mulki, wanda gwamnatin Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC suka yi kokarin gyarawa, su suka cinye wadannan shekaru bakwai da suka gabata.
“A yau a jam’iyyar APC, sojoji suna da kayan aiki, muna da jiragen yaki daga abokan huldar mu, ana fatattakar Boko Haram daga kowane bangare na kasar Najeriya, an kuma kawar da shugaban ISWAP a wani hari da jiragen Najeriya suka kai musu.”
Cikakkiyar sanarwar:
Cikakkiyar hudubar Juma’ar da ta jawo aka dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci a Apo
A wani rahoton, Legit.ng Hausa ta saurari wannan huduba ta Sheikh Nuru Khalid, ta fassara ta zuwa harshen Hausa.
Harin Jirgin Ƙasan Kaduna: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai
The Cable ta kawo asalin hudubar cikin harshen Ingilishi. “Shin babu wanda zai dauki laifi ne? Ina ganin cewa dukkaninmu mun gaza. Ma’ana – Na gaza a matsayin Limami, na gagara fahimtar da ku cewa rai na da daraja.”
“Dukkanku kun gaza a matsayinku na iyaye wajen nunawa ‘ya ‘yanku cewa kashe-kashe ba abu mai kyau ba ne. Shugabanni, ‘yan siyasa, da gwamnoni sun gaza."
Asali: Legit.ng