Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an FRSC 3 a yayin da suke bakin aiki

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an FRSC 3 a yayin da suke bakin aiki

  • Yan bindiga sun kai wani mummunan hari jihar Anambra inda suka bindige jami’an hukumar FRSC uku da ke bakin aiki
  • Lamarin ya afku ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Afrilu a yankin karamar hukumar Aguata da ke jihar
  • Jihar Anambra na fama da hare-haren yan bindiga a baya-bayan nan

Anambra - Yan bindiga sun kashe jami’an hukumar kula da hana afkuwar hadarurruka ta kasa (FRSC) uku a jihar Anambra.

Lamarin ya afku ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Afrilu a hanyar Igboukwu -Ezinifite –Uga da ke karamar hukumar Aguata da misalin karfe 2:30 na rana, jaridar The Nation ta rahoto.

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an FRSC 3 a yayin da suke bakin aiki
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an FRSC 3 a yayin da suke bakin aiki Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani ganau ya sanar da The Nation cewa ba a taba motar jami’an hukumar da aka kashe ba.

Kara karanta wannan

Kaduna: Tashin hankali yayin da mazauna suka tsinci bam a kusa da wani rafi

A ruwayar The Punch, ta ce wasu jami'an hukumar hudu sun yi nasarar tserewa cikin daji a yayin da aka kai masu farmakin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masomin lamarin

Yan ta’addan sun kona wani bangare na yankin karamar hukumar Nnewi South, Ukpor a jihar a ranar Alhamis, inda suka kashe wani mai gadi.

A ranar Juma’a, sai wasu rukuni na yan bindigar suka farmaki Amichi a Nnewi South suka kona ofishin yan sanda tare da kashe wasu jami’an yan sanda da ba a san adadinsu ba.

An tattaro cewa jami’an na FRSC suna a bakin aiki ne lokacin da harin ya wakana.

Kakakin FRSC reshen Anambra, Margret Enable, ta bayyana cewa har yanzu bata samu cikakken rahoton da zai sa ta tabbatar da lamarin ba.

Ta yi alkawarin sake waiwaya idan har ta samu cikakken labaran amma dai bata yi hakan ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Karar kwana: 'Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye

Yadda NRC ta yi watsi da gargadin da aka yi mata kan shirin kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

A wani labari na daban, hukumar kula da ayyukan jirgin kasan Kaduna sun yi karin haske kan gazawar jami’ai a matakai daban-daban wajen dakile farmakin da aka kai wa jirgin kasa, wanda aka samu gargadi tun watanni da suka gabata.

Wasikun da aka aike wa hukumomin tsaro da Daily Trust ta gani sun bayyana yadda aka bankado wannan makarkashiyar biyo bayan kutsen da jami’an leken asiri suka yi wanda ya kai ga fitar da sanarwar ga hukumomi daban-daban.

Manyan jami’an tsaro na zargin jami’an hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya NRC da kin bin shawarar da aka ba su na takaita zirga-zirgar jiragen kasa zuwa rana kadai banda dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng