Allah Ne Kaɗai Ke Bada Mulki, Kuma Ya Karɓa: Martanin Sheikh Nuru Khalid Bayan Dakatar Da Shi Daga Limanci
- A karon farko, limamin masallacin Apo Legislative Quarters Mosque, Abuja, Shiekh Nuru Khalid, ya yi magana kan dakatar da shi da kwamitin masallaci ta yi
- A sakon da ya fitar, Sheikh Khalid ya ce Allah madaukakin sarki ne kadai ke bada mulki ga wanda ya so kuma ya karba a lokacin da ya so
- Sheikh Khalid ya bukaci 'yan Najeriya su cigaba da yi wa kasarsu addu'a da shugabannin su domin samun zaman lafiya da cigaba
FCT, Abuja - Babban limanin masallacin Apo Legislative Quarters Mosque, Shiekh Nuru Khalid, wanda aka dakatar kan wa'azin da ya yi da ake yi wa kallon na 'sukar gwamnati' ya yi magana a karon farko, rahoton The Punch.
Khalid, wanda aka fi sani da Digital Imam, a cikin wani sako da ya wallafa cikin harshen larabci ya ce, "Allah ne mafi girma da buwaya. Shi ya ke bada mulki kuma ya karba daga hannun duk wanda ya ga dama lokacin da ya ga dama."
Gwamnatin Buhari ga 'yan Najeriya: Ku tarawa 'yan uwanku talakawa da harin jirgi ya shafa kudin magani
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Martanin Sheikh Nuru ya yi kama da abin da Muhammadu Sanusi ya fadi bayan tsige shi
Wannan sakon ya yi kamanceceniya da sakon da ke cikin wasikar da Sanusi Lamido II ya rubuta lokacin da aka tube shi a matsayin sarkin Kano.
Babban malamin ya kuma bukaci yan Najeriya su cigaba da yi wa kasarsu da shugabanni addu'a.
Ya ce, "Ya Allah! mai girma da buwaya, kai kake bada mulki ga wanda ka ke so, kuma ka kwace daga wanda ka ke so, ka ke daukaka wanda ka ke so kuma ka kaskantar da wanda ka ga dama, dukkan alheri na hannun ka, lallai kai ke da iko a kan komai."
A ranar 1 ga waan Afrilu ne kwamtin masallacin Apo Legislative Quarters ta dakatar da Khalid bisa wa'azin da ya yi a ranar Juma'a.
A cikin wa'azin, Khalid ya caccaki gwamnati kan gazawarta wurin samar da tsaro a kasar nan.
Malamin ya fada wa masu zabe kada su zabi duk wani dan siyasa da ba zai iya tabbatar musu da tsaron rayuka da dukiyoyinsu ba.
Wani sashi cikin hudubar da ya yi:
""Sharadin talakan Najeriya ya zama guda ɗaya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zabe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito zaɓe ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zabe,".
"Muna bukatar addu'a, muna bukatar zikiri, Wannan na da muhimmanci sosai musamman a yanzu da Najeriya ke fuskantar babban kallubale. Komai baya tafiya dai-dai. Mutane suna mutuwa. Babu tsaro a tituna mu.
"Mafi yawancin sassan kasar babu tsaro. Gwamnati a kullum ce mana ta ke yi tana iya kokarinta. Amma ba a yi mana abin da ya dace saboda muna son tsaro a Najeriya."
Bayan hakan ne kwamitin masallacin na Apo ta bayyana dakatar da Sheikh Nuru kan zarginsa da yunkurin tunzura al'umma.
Asali: Legit.ng