Sokoto: An Kama Matar Auren Da Ta Yi Garkuwa Da Yaron Makwabtan Ta Ɗan Shekara 3

Sokoto: An Kama Matar Auren Da Ta Yi Garkuwa Da Yaron Makwabtan Ta Ɗan Shekara 3

  • Rundunar ‘yan sandan Jihar Sokoto ta kama mutane 3 ciki har da wata matar aure wadanda ake zargin sun yi garkuwa da wani yaro mai shekaru 3
  • Kamar yadda rahoto ya nuna, yaron dan makwabtanta ne a Gidan Madi da ke karkashin karamar hukumar Tangaza a cikin Jihar Sokoto
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Sanusi Abubakar ya ce an kama matar ne yayin da ta yi yunkurin amsar N2m na kudin fansar yaron

Sokoto - Rundunar ‘yan sandan Jihar Sokoto ta samu nasarar damke wata matar aure da wasu mutane 2 da ake zargin sun sace yaron makwabcinta da ke Gidan Madi a karamar hukumar Tangaza cikin Jihar Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Sokoto: An Kama Matar Auren Da Ta Yi Garkuwa Da Yaro Mai Shekaru 3
An Kama Matar Auren Da Ta Yi Garkuwa Da Yaro Mai Shekaru 3 a Sokoto. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Yayin da aka gabatar da masu laifin ofishin ‘yan sandan, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Sanusi Abubakar ya ce an yi ram da ita ne yayin da ta nemi amsar kudin fansa N2m da suka bukata a hannun mahaifin yaron.

Kara karanta wannan

Abba Kyari Ya Ƙi Cin Abincin Gidan Yari, 'Yan Gidan Yarin Suna Murna Da Zuwansa

Matar ta koyi garkuwa da mutane ne ta hanyar sauraron rediyo

Ya ce matar ta koyi harkar yin garkuwa da mutane ne ta shirye-shiryen gidan rediyo wanda mutane suke bayyana yadda aka yi garkuwa da su bisa ruwayar Vanguard.

Abubakar ya bayyana cewa ta adana yaron ne a gidan ‘yan uwanta inda ta ce musu dan kishiyarta ne wacce ta yi tafiya kauye don neman magani.

Ya ce matar ta sauya muryarta zuwa ta namiji ta wayarta inda ta sanar da mahaifin yaron cewa dansa yana hannunta kuma matsawar ya kasa biyanta N2m za ta halaka shi.

Yayin amsar kudin fansar ne aka kama ta

A kokarinta na amsar kudin ne jami’an ‘yan sanda suka kama ta inda suke zarce da ita Hedkwatar rundunar ‘yan sanda don a ci gaba da bincike akanta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta saya wa NDLEA na'urar gane mutum idan ya sharara karya

Har ila yau an gabatar da wasu masu balle kofofi ga hedkwatar inda aka bayyana yadda suka balle asibitin jihar sannan suka sace tsadaddun abubuwa har da na’urorin sanyaya wuri guda 4.

An kama mutane biyun da abubuwan da suka sace kuma ‘yan sanda sun ce za a gurfanar da su kotu da zarar an kammala bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164