'Yan Ta'adda Sun Ji Ba Daɗi Yayin Da Sojoji Suka Kashe Fiye Da 85 a Kaduna, Zamfara Da Borno
- Dakarun sojojin Najeriya sun ce sun halaka yan ta'adda fiye da 85 a yayin wasu hare-hare da suka kai a Zamfara, Kaduna da Borno
- Kakakin rundunar sojojin saman Najeriya, NAF, ya tabbatar da hakan inda ya ce sun kai hari a dazukan Sangeko a Zamfara da dajin Kasasu a Kaduna
- Majiyoyi daga rundunar sojojin Najeriya sun tabbatar da nasarorin da sojojin suka samu na kawar da yan ta'addan da kuma kwato makamai da dama
Domin cika umurnin Shugaba Muhammadu Buhari na kawar da dukkan yan bindiga da yan ta'adda da ke adabar yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabas, jirgin yakin NAF da sojoji sun kashe yan ta'adda fiye da 85 a Zamfara, Kaduna da Borno.
A wasu hare-haren da suka kai, Sojojin Saman Najeriya sun kai hare-hare a dajin Sangeko a Zamfara da dajin Kusasu a Jihar Kaduna inda suka kashe fiye da yan ta'adda 50, rahoton Vanguard.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin NAF ya tabbatar da kai harin amma ya ce makasudin atisayen shine kara ragargazan yan ta'adda da ke arewa maso gabas da arewa maso yamma, da nufin samar da zaman lafiya a yankin.
Majiyoyi daga rundunar soji wanda suke cikin wadanda suka kai harin sun ce a Zamfara, dakarun Operation Hadarin Daji sun yi ruwan bama-bamai a dajin Sangeko, hakan yasa aka kashe kimanin yan ta'addan 50 da aka hange su kan babura suna shirin kai hari.
Bayan tabbatar da wurin taron yan ta'addan da fasahar ISR, an umurci jirgin yakin NAF ya kai hari a wurare daban-daban tare da wasu jami'an tsaro.
Hakazalika, an sake yi wa yan ta'addan da aka hangi suna tserewa daga harin na farko ruwan wuta, an kawar da su.
A dajin Kusasu, binciken da NAF ta yi da na'urar ISR daga ranar 30 zuwa 31 na watan Maris, ya tabbatar da yan ta'addan suna zirga-zirga suna barin dajin a cikin dare.
Daga bisani, jirgin na NAF ya yi musu ruwan wuta a dajin, an gano gawarwaki fiye da 30 yayin da wasu daga cikinsu sun tsere.
An ragargadi yan Boko Haram a arewa maso gabas
A arewa maso gabas, bayan gano mabuyar yan ta'addan a Tumbuns kusa da Bukar Meram da Kollaram inda yan Boko Haram ke taruwa, sojojin kasa da NAF sun kai wa yan ta'addan hari.
Harin ya tarwatsa wurin haduwar na yan ta'addan tare da kashe wasu da dama cikinsu, yayin da daga bisani an gano makamai masu yawa da suka boye domin su kai hari.
Asali: Legit.ng