Kada ku zabi duk dan yan siyasan dace matasa suka siya masa fam, Obasanjo
- Tsohon Shugaban Obasanjo ya baiwa yan Najeriya satar amsa kan masu neman kujerar shugaban kasa a 2023
- Obasanjo wanda ya mulki Najeriya sau biyu daga 1999 zuwa 2007 yace yawancin yan takaran na yiwa Najeriya karyan saya musu fam akayi
- Kusan dukkan yan takaran da suka bayyana niyyar takara kawo yanzu sun ce wasu matasa ne suka saya musu Fam din takara
Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, jiya ya yi kira ga yan Najeriya kada su zabi duk dan takaran da yayi karyan cewa wasu matasa ne suka saya masa Fam din takara.
A cewar Obasanjo, wannan shine hanyar farko na gane masu yaudarar jama'a kuma ya zama dole a tona musu asiri.
Obasanjo ya bayyana hakan a jihar Legas yayin taron murnar cikar Fasto Itua Ighodalo, shekaru 61, rahoton Leadership.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, matsalar Najeriya daya ce, kuma itace shugabanci.
Yace:
"Yau, suna biyan N40m. Wasu na cewa wasu matasa ne suka saya musu. Kai, duk wanda ya muku wannan karyan kada ku zabeshi. Wasu matasa suka tara N40m? Idan kana son siya, ka siya. Babu bukatar yi mana karya."
"Idan ka tambayeni menene matsalar Najeriya, shugabanci ce. Idan ka tambayeni menene mafita, shugabanci ne."
A cewarsa, ko Najeriya ta tattara dukkan kundin tsarin mulki mafi kyau a duniya, idan ba'a samu mutanen kirkin da zasu aiwatar da su ba, babu wata cigabar da za'a samu.
Sabon Rikici: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya yi barazanar maka PDP a Kotu kan kuɗin Fam
Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Ayoola Falola, ya bayyana makudan kuɗin da jam'iyya ta sa na kuɗin nuna sha'awa da son zuciya don masu kuɗi.
Leadership ta rahoto cewa ɗan takarar ya yi barazanar ɗaukar matakin doka kan jam'iyya, "idan ba'a yi gaggawar shawo kan lamarin ba kuma aka ƙi yin adalci."
Falola, wanda ya yi bayanin shi mamba ne na PDP a gunduma ta 12, karamar hukumar Ibadan South West a jihar Oyo, ya tura korafi kai tsaye ga shugabancin jam'iyya na ƙasa.
A cewarsa, makudam kuɗin da aka sa wa Fam ɗin bai yi kama da matsanancin rashin kuɗin da ake fama da shi a Najeriya ba a yanzu.
Asali: Legit.ng