Tsawon Shekaru 6 Ƙaramar Hukuma Ta Tana Ƙarkashin Ikon Boko Haram, Kakakin Majalisar Borno Ya Koka
- Abdulkareem Lawan, Kakakin majalisar jihar Borno ya bayyana cewa tsawon shekaru shida karamar hukumarsa ta Guzamala tana hannun Boko Haram
- Lawan ya bayyana hakan ne yayin wani taro na bawa daliban mazabansa tallafin kudi ga wadanda ke karatu a makarantun gaba da sakandare
- Kakakin majalisar ya mika rokonsa ga gwamnatin tarayya da rundunar sojoji da a gaggauta atisayen kawar da yan ta'addan domin mutanensa su koma gida
Borno - Kakakin majalisar jihar Borno, Abdulkareem Lawan ya koka kan yadda har yanzu yan ta'addan ISWAP ke rike da iko a karamar hukumarsa ta Guzamala, hakan yasa mutane da sojoji suka fice daga nan.
Kakakin ya yi wannan jawabin ne yayin rokon gwamnatin tarayya da sojoji su yi amfani da damar atisayen Operation Desert Sanity da Operation Hadin Kai ta kaddamar don kawar da yan ta'adda daga yakin Tafkin Chadi.
Ya ce wannan zai taimaka wa mazauna garuruwan su koma gidajensu su cigaba da rayuwa yadda suka saba kamr yadda The Punch ta rahoto.
Ya yi wannan rokon ne a ranar Juma'a yayin bikin kadamar da bada tallafin karatu na Naira miliyan 5 ga yan asalin Guzamala su 446 da ke karatu a makaratun gaba da sakandare.
An yi wannan bikin ne a dakin taro na Sir Kashin Ibrahim a Kwallejin Ilimi ta Maiduguri, Jihar Borno.
"Dukkan karamar hukumar Guzamala inda na fito tana karkashin Boko Haram ne kuma babu sojoji domin yan ta'addan sun kore su shekaru shida da suka gabata. A yanzu, Kukawa, wanda shine hedkwatar karamar hukumar Kukawa ne kadai akwai sojojin Najeriya kuma babu farar hula.
"Babu ko farar hula daya a Guzamala, balantana sojoji da hedkwatar karamar hukumar da garuruwan da ke kewaye da shi, mutanen mu har da hakimai suna sansanin yan gudun hijira da garuruwa kamar Nganzai, Monguno da wasu kananan hukumomi da ke makwabtaka ciki har da Maiduguri tsawon shekaru shida.
"Mutanen mu sun kosa su koma gida, abin takaici ne ganin wannan ba shine karo na farko da na ke naman a kawo sojoji Guzamala ba da kewaye domin mutanen garin mu su amfana da aikin da Gwamna Zulum ke yi na mayar da mutane garuruwansu, amma har yanzu shiru. Ina sake nanatawa cewa Guzamala baya shiguwa," in ji Lawan.
Kakakin ya yi kira ga gwamnatin tarayya da rundunar sojoji su gaggauta atisayen da sojoji ke yi na Desert Sanity don mayar da mutane Guzamala da Kukawa da har yanzu suke hannun Boko Haram.
A jawbinsa, kakakin majalisar ya gode wa sojojin bisa kokarinsu na yaki da yan ta'addan da sauran miyagu a yankin na arewa maso gabas baki daya.
Lawan ya ce ya dade yana bada tallafi ga dalibai yan asalin jihar ta ke karatu a manyan makarantu a jihar da wasu jihohi ma baya ga ayyukan mazaba.
'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci
A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.
A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.
Asali: Legit.ng