Tunatarwa: Abubuwan da ya kamata kusani masu muhimmanci kafin fara Azumin Ramadan
- Azumtar watan Ramadana na ɗaya daga cikin abubuwa 5 da aka gina Musulunci a kan su kuma shi ne wata na Tara
- Kowane Musulmi an umarce shi ya Azumci watan na kwana 29 ko 30, amma akwai wasu rukunin mutane da Allah ya musu rangwame
- Mun tara muku muhimman abubuwa game da watan Ramadan da ya dace ku sani kafin shigowarsa
Ramadan na ɗaya daga cikin ginshiƙan Addinin Musulunci guda biyar kuma shi ne wata na 9 a cikin jerin watannin Musulunci guda 12.
Musulmai na farin ciki da watan kasancewar a cikinsa ne aka fara yi wa Annabi Muhammad (SAW) wahayi na farko na littafi Mai tsarki Alƙur'ani.
A wannan watan Musulmai na ƙara gyara halayen su kuma su ƙara matsawa kusa da Ubangijinsu, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Suna Azumi ne ta hanyar daina cin abinci da sham abin sha, shan kwayoyi da kuma kame wa daga saduwa da matansu na tsawon kwana 29 ko 30.
Haka nan kuma an so Musulmai su nisanci aikata laifuka kamar maganar wani a bayan idonsa a tsawon watan Ramadan.
Wata ne na Azumi, Addu'a, ƙanƙan da kai ga Allah, karanta Alkur'ani, tsaftace zuciya da rai, bada sadaƙa, soyayya. hakuri da sauran kyawawan halaye da Allah ke so.
Yaushe ake fara Ramadan?
Farawa da kuma ƙarshen watan Ramadan ya jingina ne da yadda Kalandar Addinin Musulunci take tafiya a kowace shekara da kuma ganin jinjirin wata.
Musulmai na ɗaukar Azumin farko na watan Ramadan ne bayan shugabannin Addinin Musulunci na ƙasashen duniya sun danar da ganin wata.
A wannan shekarar ana hasashen za'a fara Azumi ranar 1 ga watan Afrilu, 2022 kuma a kammala shi ranar 1 ga watan Mayu, 2022 tare da murnar karamar Sallah (Eid El-Fitr) a washe gari.
Majalisar ƙoli ta Addinin musulunci (NSCIA) a Najeriya ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ranar Alhamis, ta umarci musulmai su fara duban jinjirin watan Ramadan ranar Jumu'a (yau).
Wane Musulmi ne zai yi Azumi?
Kowane Musulmi, ban da mara lafiya, matafiyi, tsohon da ya jigata, mace mai shayarwa, da mai jinin haila, zasu yi Azumin watan Ramadan.
Su waye Azumi bai hau kansu ba?
Kancewar Ramadan wata ne mai daraja a Kalandar Musulunci, mabiya addinin Musulunci na matuƙar son zuwansa a dukkan sassan duniya. Wata ne mai rahama da gafara da babu kamarsa.
Akwai waɗan da Allah bai wajabta Azumi a kansu ba, sun haɗa da; ƙananam yara da basu kai lokacin balaga ba, tsofaffi, marasa lafiya da wanda ya rasa hankali, mai juna biyu. mai shayarwa da matafiya.
A wani labarin kuma Shin kunsan ƙasashen da Musulmai zasu yo dogon Azumi na tsawon watanni da wanda zasu yi gajere a Bana?
Biliyoyin al'ummar Musulmai a faɗin duniya na gab da shiga wata mai Albarka Ramadan na shekarar 2022.
Musulman wasu ƙasashe za su fuskanci dogon Azumi na tsawon awanni a bana, yayin da wasu kuma za su yi gajere.
Asali: Legit.ng