Tashin hankali: Zanga-zanga ta barke bayan da tsawa ta kashe matasa 4 a Ondo
- Wasu matasa sun tada hankalin jama'a bayan da iftila'in tsawo ya hallaka wasu matasa hudu a yankin Akure
- Wannan lamari ya haifar da firgici, har ta kai ga wasu matasa suka fara zanga-zanga a yankin na jihar Ondo
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar mutuwar mutanen hudu, kana ta musanta faruwar zanga-zangar
Akalla matasa hudu ne aka ce iftala'in tsawa ta kashe a Ago Dada, a karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa, matasan sun mutu ne a yammacin Larabar da ta gabata yayin da aka yi ruwan sama a kauyen.
Wata majiya ta shaida cewa, mutuwar matasan ta haifar da zanga-zanga a kauyen a ranar Alhamis, wanda ya yi sanadin mutuwar wani dattijo tare da lalata dukiyoyi daga fusatattun matasan.
A cewar majiyar, abin bakin cikin matasan shi ne, matattun hudu da tsawa ta kashe duk ba ‘yan asalin yankin bane.
Ya kuma kara da cewa, wadanda ba ‘yan asalin kauyen ba da suka fusata da lamarin, sun yanke shawarar kai wa ‘yan asalin kauyen hari tare da lalata musu dukiyoyin su.
Ya bayyana cewa:
“Matasan kauyen sun dauki makami a safiyar yau (Alhamis) wanda yayi sanadiyar kashe wani dattijo a kauyen. Babban abin da matasan suka damu dashi shi ne cewa matasan hudu da suka mutu duk ba ‘yan asalin kauyen bane. An lalata wasu gine-gine na ’yan asalin Akure."
Da take tabbatar da faruwar lamarin yayin da aka tuntubi rundunar ‘yan sanda, Misis Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta musanta cewa an yi zanga-zanga a kauyen.
Odunlami ta ce:
“Zan iya tabbatar muku da cewa tsawa ta kashe matasa hudu a kauyen, amma babu wata zanga-zangar da ta kai ga mutuwar wani a kauyen.
"Watakila an yi gardama ne a lokacin da iyalan wadanda abin ya shafa suka so dauko gawarwakin wadanda abin ya shafa don binne su. Abu ne mai matukar zafi, amma ga wa za su yi wa zanga-zangar?
Yan bindiga sun Kone Sakatariyar karamar hukuma a jihar Anambra
Mutane sun shiga tashin hankali mara misaltuwa ranar Alhamis yayin da yan bindiga suka ƙona Sakatariyar ƙaramar hukumar Nnewi South, jihar Anambra.
Punch ta rahoto cewa zuwa yanzun an tabbatar da mutum ɗaya ya rasa rayuwarsa yayin mummunan lamarin da safiyar nan.
Duk da ba'a gama tantance yawan mutanen da lamarin ya shafa ba, amma ana zaton wanda ya mutu shi ne mai gadin Sakatariyar.
Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da cewa mutum da ya rasa ransa yayin harin Mai gadin Sakatariyar ne, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Murna Ta Koma Ciki: Tsawa Ta Hallaka Yan Bikin Aure 17 Ana Tsaka da Cashewa, Ango Ya Jikkata
A wani labarin, hukumomi a ƙasar Bangaladesh sun bayyana cewa aƙalla mutum 17 cikin mahalarta wani bikin aure ne suka rasa rayukansu sanadiyyar wata tsawa mai karfi.
Rahoto ya nuna cewa wasu 14 sun jikkata, cikinsu harda mai gayya wato Ango, sai dai amarya ba ta samu halartar wurin cashewar ba.
BBC Hausa ta ruwaito cewa an shirya shagalin bikin ne a cikin wani jirgin ruwa na musamman dake kusa da tekun Shibganj.
Asali: Legit.ng