Murna Ta Koma Ciki: Tsawa Ta Hallaka Yan Bikin Aure 17 Ana Tsaka da Cashewa, Ango Ya Jikkata

Murna Ta Koma Ciki: Tsawa Ta Hallaka Yan Bikin Aure 17 Ana Tsaka da Cashewa, Ango Ya Jikkata

  • Wata tsawa ta hallaka akalla mutun 17 cikin mahalarta wani shagalin biki ana cikin cashewa
  • Lamarin ya faru ne a cikin wani jirgin ruwa dake kusa da tekun Shibganj a kasar Bangaladesh
  • Wasu mutum 14 sun jikkata cikinsu harda Ango yayin da ita amarya ba ta samu halartar wurin shagalin bikin nasu ba

Bangaladesh:- Hukumomi a ƙasar Bangaladesh sun bayyana cewa aƙalla mutum 17 cikin mahalarta wani bikin aure ne suka rasa rayukansu sanadiyyar wata tsawa mai karfi.

Rahoto ya nuna cewa wasu 14 sun jikkata, cikinsu harda mai gayya wato Ango, sai dai amarya ba ta samu halartar wurin cashewar ba.

BBC Hausa ta ruwaito cewa an shirya shagalin bikin ne a cikin wani jirgin ruwa na musamman dake kusa da tekun Shibganj.

Tsawa ta kashe mutum 17
Murna Ta Koma Ciki: Tsawa Mai Karfi Ta Hallaka Yan Bikin Aure 17 Ana Tsaka da Cashewa, Ango Ya Jikkata Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Tsawar ta faɗa musu kashi-kashi

Tsawar ta afkawa mahalarta bikin ne yayin da suke cikin jirgin ruwan a kan hanyarsu ta zuwa gidan Amarya.

Wasu mutane da suka ga lokacin da lamarin ya faru sun bayyana cewa tsawar ta faɗa wa jirgin ne kashi-kashi.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS ta karyata zarginta da ake na tsare mutane ba bisa ka'ida ba

Wasu shaidun gani da ido suka ce:

"Kashi-kashi na tsawar ne ya afka cikin jirgin da mahalarta shagalin bikin suke ciki."

Legit.ng hausa ta gano cewa wannan ba shi ne na farko ba, kuma daman tsawa na yawan hallaka mutane a faɗin kudancin Asiya.

A wani labarin na daban gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya bayyana cewa yana goyon bayan tsarin mulkin karba-karba a Najeriya.

Da yake jawabi game amfanin tsarin, Gwamna Sule, yace irin wannan tsari ne ya kai shi ga ɗarewa kujerarar gwamna a jihar Nasarawa.

Ya kuma kara da cewa a duk lokacin da aka kai mulki ga wani yanki sai a zaɓo wanda mutane suka amince da shi a wannan yanki a tsayad da shi takara.

Sai dai yace wannan ra'ayin shi na ƙashin kaine ba wai na gaba ɗaya gwamnonin jam'iyyar APC bane, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An Cafke Wani Dalibin Jami'a Ya Yi Shigar Mata Ya Zauna Jarabawar Budurwarsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel