Kaduna: Tashin hankali yayin da mazauna suka tsinci bam a kusa da wani rafi
- Wasu bata-garin 'yan bindiga sun nufi al'ummar yankin jihar Kaduna da sharri, amma Allah ya kubutarsu
- An samu nasarar ganowa tare kunce wani bam da aka dasa a kusa da wani rafi a yankin Rigasa na jihar Kaduna
- A baya dai an samu irin wannan barna na 'yan bindiga, inda bam din ya jikkata wani mai sana'ar POS
Kaduna - Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta dakile yiwuwar tashin wani harin bam da aka dasa a yankin Shanono da ke unguwar Rigasa a karamar hukumar Igabi a jihar.
Rahotanni sun ce an boye na’urar ne a cikin wani bokiti kana aka jefar da kusa da wani rafi da misalin karfe 6:30 na safiyar ranar Alhamis 31 ga watan Maris.
Wani mazaunin yankin mai suna Tijjani Haruna Shehu ya shaida wa Daily Trust, cewa an rufe bokitin ne da salatef wanda ya sa mutanen da ke kusa da wurin suka fara nuna shakku.
A cewarsa:
“An boye na’urar ne a cikin bokitin roba da aka lullube da salatef wanda ya sa muka yi zarginsa. Nan take shugabannin al’ummar mu suka sanar da ‘yan sanda ciki har da DSS kafin jami’an da ke yaki da bama-bamai su zo su kunce shi."
A cewarsa, akwai wayoyi da aka sarkafa a cikin bokitin da aka rufe.
Daruruwan mazauna garin ne suka hallara domin shaida yadda ‘yan sandan suka kunce na’urar da ta haifar da firgici.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Jalige Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi karin bayani ba.
An ruwaito a makon da ya gabata yadda wani mai POS ya samu rauni a lokacin da wani bam ya fashe a kusa da babur dinsa a unguwar Rigasa.
Na'urar ta biyu dai rundunar da ke aikin kunce bama-bamai na jihar Kaduna sun yi nasarar hana ta tashi.
Jirkin yakin sojojin Najeriya ya halaka yan ta'adda 34 a bodar Kaduna da Neja
Jirgin yaƙin rundunar sojin Najeriya ya gano tare da aika yan ta'adda 34 lahira a ƙauyen Mangoro, yankin da ya yi iyaka tsakanin jihar Kaduna da Neja.
Leadership ta rahoto cewa Sojin sun samu bayanin cewa an ga yan ta'adda kusan 70 a kan Babura 40 da wasu a ƙafa sun nufi hanyar Akilibu – Sarkin Pawa, a ranar 30 ga watan Maris.
Majiya daga cikin dakarun sojin ya bayyana cewa bayan samun bayanan sirri na yan ta'adda, Dakarun sojin sama na Operation Thunder Strike, suka tashi jirgi ya bibiyi lamarin kuma ya musu luguden wuta.
A wani labarin kuma Yan bindiga sun ƙone Sakatariyar karamar hukuma a jihar Anambra.
Wasu yan bindiga sun kona Sakatariyar karamar hukumar Nnewi South a jihar Anambra, mutum ɗaya ya rasa rayuwarsa.
Wani shaida ya tabbatar da cewa Mai gadin wurin ne ya mutu, mutane sun shiga yanayin tashin hankali a yankin.
Asali: Legit.ng