Karin bayani: 'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, sun kashe 9 a jihar Neja
- Rahotannin da ke shigowa daga jihar Neja sun bayyana cewa, an hallaka wasu jami'an tsaro tara a harin 'yan bindiga
- Rahoton ya ce, an yiwa jami'an tsaron ne kwanton bauna, inda aka hallaka su ba tare da wani shiri ba
- Lamurran rashin tsaro dai na kara ta'azzara a Najeriya, musamman a yankin Arewa masu Yammacin Najeriya
Jihar Neja - Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari kauyukan Kabo da Shako da ke karamar hukumar Gurara a jihar Neja, inda suka kashe jami’an tsaro har tara.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyuka 11 a yammacin ranar Talata 29 ga watan Maris a jihar ta Neja.
Sai dai, hare-haren da aka kai a Kabo da Shako sun yi matukar muni, lamarin da ya kai ga zubar da jini yayin da 'yan ta'addan suka yi wa jami’an tsaro kwanton bauna, suka kashe tara daga cikinsu.
An tattaro cewa jami’an da aka kashe sun hada da sojoji da ‘yan sanda da kuma ‘yan banga da ke yankin domin amsa kiran gaggawa don magance matsalolin tsaro.
An ruwaito cewa al’ummar na zaune ne a yankunan karkarar Dikko mai tazarar kilomita kadan da babban birnin tarayya Abuja.
'Yan bindiga sun halaka jama'a masu yawa a sabon harin da suka kai Benue
An kashe mutane uku a wani farmakin da aka kai garin Naka da ke karamar hukumar Gwer ta yamma a jihar Benue.
Harin ya faru sa’o’i 24 bayan kashe wani Faston cocin Deeper Life da wasu mutane uku a karamar hukumar Guma da ke jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Naka, wani gari kasuwanci na karkara kuma hedkwatar karamar hukumar Gwer ta Yamma, ya zama mai masaukin baki ga ‘yan gudun hijira daga kauyukan yankin.
Majiyoyi sun ce sabon harin da aka kai a garin ya faru da misalin karfe 8 na daren ranar Talata.
Wani mazaunin garin ya ce mutane sun fara gudu ta biyo bayan karar harbe-harbe da aka yi a kusa da Kwalejin Comprehensive da ke Naka.
Ba a gama jimamin harin jirgin kasa ba, 'yan bindiga sun hallaka mutum 23 a Kaduna
A wani labarin, wasu ‘yan bindiga sun sake kashe wasu mutane 23 tare da raunata wasu da dama a wasu kauyuka biyu na karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.
Wannan dai shi ne hari na hudu a jere da ‘yan bindiga suka kai a cikin mako guda a kauyukan karamar hukumar, Daily Trust ta ruwaito.
Kauyukan da ‘yan bindigar suka kai hari sun hada da Anguwar Maiwa da Anguwar Kanwa.
Asali: Legit.ng