Karin bayani: Baya ga Azman, kamfanin jirgin Air Peace ya dakatar da aiki a Kaduna
- Rahotanni da ke shigowa na bayyana yadda kamfanonin sufurin jiragen sama sun fara daukar matakin dakatar da ayyukansu a Kaduna
- Kamfanin Air Peace ya bayyana dakatar da ayyukan jiragensa a jihar Kaduna jim kadan bayan da kamfanin Azman ya dauki irin wannan mayaki
- Wannan na zuwa ne bayan da wasu 'yan bindiga suka dumfari tashar jirgin saman jihar Kaduna a karshen makon jiya
Kaduna - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, kamfanin jiragen sama na Air Peace ya dakatar da ayyukansa zuwa filin jirgin sama na Kaduna.
Wata majiya ta alakanta faruwar lamarin ga harin da aka kai a kusa da filin jirgin Kaduna a karshen makon jiya.
Idan baku manta ba, an ruwaito yadda wasu ‘yan bindiga suka bindige wani mai gadi da ke aiki a hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya a ranar Asabar.
Sojoji sun yi artabu da ‘yan ta’addan, lamarin da ya janyo tsaikon tashin jirgin sama na Azman da ke kan hanyarsa ta zuwa Legas, kamar yadda Punch ta tattaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar Talata ne Azman ya sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragensa zuwa Kaduna har sai baba ta gani saboda rashin tsaro a yankin.
Bayan sa’o’i kadan ne aka samu labarin dakatar da ayyukan jiragen Air Peace zuwa Kaduna.
Harin filin jirgin saman Kaduna: 'Yan bindiga tserewa suka yi da ganin jami'anmu, gidan soja
A wani labarin na daban, hukumar soji a ranar Litinin, 28 ga watan Maris, ta bayyana cewa yan bindiga basu isa su kai farmaki filin jirgin sama na Kaduna ba.
Da take martani kan kisan wani jami’in hukumar NAMA, rundunar tace lamarin ya faru ne kimanin kilomita shida dagatashar jirgin da kuma wajen katangar filin jirgin.
Da yake jawabi ga manema labarai a wajen harin, kwamandan rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Uriah Opuene, ya ce filin jirgin na Kaduna na da tsaro sosai.
Asali: Legit.ng