Harin jirgin Abuja-Kaduna: Mun garzaya da wadanda suka jikkata asibiti: Gwamnatin Kaduna

Harin jirgin Abuja-Kaduna: Mun garzaya da wadanda suka jikkata asibiti: Gwamnatin Kaduna

  • Gwamnatin Kaduna ta bayyana abinda tayi yayinda ta samu labarin abinda ya faru da jirgin kasan Abuja-Kaduna
  • Wani dan'uwan wanda abin ya shafa ya ce dan'uwansa ya rasa ransa a harin
  • Yayinda ta tabbatar da wasu sun jikkata, bata bayyana adadinsu ba kuma bata ce an yi rashin rai ba

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana halin da ake ciki game da harin Bam din da aka kaiwa layin dogon Abuja zuwa Kaduna ranar Litinin, 28 ga watan Maris, 2022.

Kwamishanan tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan, a jawabin da ya saki ya bayyana cewa jami'an Sojoji sun dira wajen kuma suna tsare fasinjojin.

Harin jirgin Abuja-Kaduna
Harin jirgin Abuja-Kaduna: Mun garzaya da wadanda suka jikkata asibiti: Gwamnatin Kaduna Hoto: DailyNigerian
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Obi na Onitsha: Amsa waya ya hana ni hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa farmaki

A cewarsa, an kwashe fasinjojin daga cikin dajin zuwa ckin gari yayinda aka garzaya da wadanda suka jikkata asibiti.

Yace:

"Gwamnatin jihar Kaduna ta samu rahotannin hari da aka kai jirgin Abuja-Kaduna wajen Kateri-rijana."
"Da wuri aka tuntubi jami'an tsaro kuma aka tura jami'ai don tsare fasinjojin dake wajen. Ana kokarin kwashe fasinjojin daga wajen kuma an kai wadanda suka ji rauni asibiti."

Wakilin AriseNews, Nissi Gabriel, a rahoton da ya koro daga Kaduna ya bayyana cewa wani nakusa da wadanda abin ya shafa yace sun yi rashin dan'uwansu a hari.

Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Ado Doguwa, ya ce ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu duba da tabarbarewar tsaro a kasar nan.

Dan majalisar wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada ta Kano ya bayyana haka ne a zaman da majalisar ta yi a yau Alhamis a lokacin da ake muhawara kan harin da ‘yan ta’adda suka kai kan wani jirgin kasan fasinja a garin Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye da bayanan mutanen da suka mutu a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Doguwa, wanda wannan mummunan al’amari ya kai shi zub da hawaye, yana kan ra’ayin cewa jami’an tsaro sun gaza, don haka bai kamata ‘yan kasa su ci gaba da zama cikin cutarwar ‘yan ta’adda ko ‘yan fashi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng