Sojoji sun yi kaca-kaca da maboyar 'yan ta'addan IPOB, sun kwato muggan makamai

Sojoji sun yi kaca-kaca da maboyar 'yan ta'addan IPOB, sun kwato muggan makamai

  • Dakarun sojin Najeriya na sashi na 82 sun fatattaki mabuyar yan awaren IPOB da mayakanta na Eastern Security Network
  • Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar sojin ya tabbatar da ci gaban a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, 28 ga watan Maris
  • Mabuyar ita ce sansanin Innocent Obieke (wanda aka fi sani da Double Lion), wanda aka ce shine shugaban yan banga a yankin

Anambra - Rundunar sojin Najeriya ta farmaki mabuyar ta’addanci na kungiyar yan awaren IPOB da mayakanta na Eastern Security Network ( ESN) a Orsumoghu, karamar hukumar Ihiala da ke jihar Anambra.

A wata sanarwa daga Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar sojin, ya yi bayanin cewa tsagerun kungiyoyin sun kai hare-haren ta’addanci kan al’umman da basu ji ba basu gani ba tare da kai farmaki ga hukumomin tsaro daga mabuyarsu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ma'aikatan jami'a karkashin SSANU da NASU sun hargitsa jami'ar Legas

Sojoji sun yi kaca-kaca da maboyar 'yan ta'addan IPOB, sun kwata muggan makamai
Sojoji sun yi kaca-kaca da maboyar 'yan ta'addan IPOB, sun kwata muggan makamai Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

A yayin da suke gudanar da aikin kakkaba a garuruwan kan iyaka, sojojin sun fuskanci turjiya mai tsanani daga 'yan adawa, yayin da suka kutsa cikin mabuyar tasu.

Ya ce dakarun sojin sun sha kansu bayan sun bude masu wuta, inda suka tursasa su barin mabuyarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan sun bar sansaninsu, sai dakarun sojin suka ci gaba da kai farmaki sannan suka kwato tarin makamai da suka hada da bindigohi da adduna.

Sauran kayayyakin da suka kwato sun hada da wayoyi iri-iri, layukan waya, na’ura mai kwakwalwa, motar Hilux daya da layoyi.

Bincike ya nuna mabuyar ita ce sansanin Innocent Obieke (wanda aka fi sani da Double Lion), wanda aka ce shine shugaban yan banga a yankin, amma yana aiwatar da ayyukan ta’addanci.

Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su ci gaba da ba dakarun da sauran hukumomin tsaro goyon baya da bayanai a kan lokaci domin a samu kama masu laifuka a yankin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun kai mummunan hari Hedkwatar yan sanda, mutane sun yi takansu

Yan sanda sun kashe yan bindiga 4, sun gano bama-bamai 5 da ba a tayar ba

A wani labarin kuma, rundunar yan sandan jihar Imo ta kashe yan bindiga biyar da ake zaton yan kungiyar awaren IPOB ne a wani musayar wuta da suka yi a safiyar Lahadi, 20 ga watan Maris.

Lamarin ya faru ne lokacin da yan bindigar suka je kai farmaki ofishin yan sanda da ke karamar hukumar Oru East a jihar Imo.

Kakakin yan sandan jihar, Micheal Abattam, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Owerri, babbar birnin jihar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng