An bada umirnin rufe ofishohin gwamnati karfe 1 gobe don bada daman kallon wasar Najeriya da Ghana
- Yan wasan kwallon Najeriya Super Eagles zasu buga wasa mai muhimmanci ranar Talata a kasar Ghana
- Saboda muhimmacin wannan wasa, gwamnatin tarayya ta saki sakon kar ta kwana
- Najeriya ta tashi da Ghana a birnin Kumasi makon da ya gabata ba ci, wannan shine wasan raba gardama
Gwamnatin tarayya ta bada umurnin rufe dukkan ma'aikatun gwamnati karfe daya ranar Talata don baiwa mutane daman shirya zuwa halartan wasan kwallon Najeriya da Ghana.
Za'a buga wasa kwallon hayewa gasar kofin duniya a Qatar 2022 ranar Talata a filin kwallon Moshood Abiola dake birnin tarayya Abuja.
Alkawarin Ahmed Musa ga 'yan Najeriya: Za mu lallasa Ghana domin shiga gasar cin kofin duniya na 2022
Ahmed Musa ya bayyana cewa ‘yan wasan kwallon kafan Najeriya; Super Eagles za su yi iya kokarinsu wajen ganin sun gamsar da ‘yan Najeriya ta hanyar samo tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022, inda ta alkawarta lallasa Ghana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kyaftin din na Super Eagles ya ce 'yan wasan Najeriya sun yi nadamar rashin tabuka abin a zo a gani a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Senegal ta lashe watannin baya, Sports Brief ta tattaro.
Musa da yake zantawa da tashar Youtube ta hukumar kwallon kafa ta Najeriya ya yi gargadin cewa wasan da Super Egales za ta buga tsakaninta da Black Stars zai kasance mai wahala saboda hamayyar da ke tsakanin Najeriya da Ghana.
Asali: Legit.ng