Hasashen Shehu Sani: Abubuwan da Abba Kyari zai yi gamo dasu a magarkamar Kuje
- Sanata Shehu Sani ya yi magana kan barazanar da DCP Abba Kyari ke iya fuskanta yayin da kotu ta bayar da umarnin a mayar da shi gidan yari a ranar Litinin, 28 ga Maris
- Tsohon dan sanatan ya ce fursunonin da Kyari ya taba kamawa na iya lakada masa duka ko aikata munanan ayyuka a kansa a gidan yarin
- Domin kaucewa irin wannan yanayi, Sanata Sani ya ce masu kula da gidan yari ya kamata su ajiye Kyari da ke fuskantar tuhumar safarar miyagun kwayoyi a wani dakin na daban
Sanata Shehu Sani, tsohon dan majalisar dattawan Najeriya, ya yi tsokaci kan abin da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari zai iya fuskanta a gidan yari.
Sani wanda dan takarar gwamna ne a karkashin jam’iyyar PDP ya bayyana haka ne bayan wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta bayar da umarnin mika Kyari zuwa gidan gyaran hali na Kuje a ranar Litinin, 28 ga watan Maris.
DCP Kyari da wasu mutane shida na fuskantar tuhumar safarar miyagun kwayoyi daga hukumar NDLEA ta Najeriya.
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Sanata Sani ya ce ya dai kamata a ajiye babban jami'in 'yan sandan da aka dakatar a wani dakin na daban domin kubutar da shi daga duka ko cutarwar fursunonin gidan yarin da ya taba kamawa.
Rubutun da ya yi a Twitter ya bayyana cewa:
“Lokacin da aka ba da umarnin tsare dan sanda a gidan yari, abin da ka fara damun jami’an gidan yarin shi ne yadda za su kare shi daga fursunonin da ya taba kamawa aka kai su gidan yari, a yanayi irin wannan, akan a ajiye shi a wani daki na daban domin ceton shi daga dukan tsiya ko kuma a cutarwa."
Kotu ta ki amincewa da ba da belin DCP Abba Kyari
A wani labarin, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar neman belin da DCP Abba Kyari da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Sunday J. Ubua suka shigar.
Idan baku manta ba ana tuhumarsu da laifukan da suka shafi harkallar muggan kwayoyi tare da wasu mutane biyar, The Nation ta ruwaito.
Mai shari’a Emeka Nwite, a wani hukunci da ya yanke a safiyar yau Litinin, ya ce masu gabatar da kara sun gabatar da isassun hujjoji a gaban kotu domin nuna kin amincewa da belin manyan jami’an ‘yan sandan biyu.
Asali: Legit.ng