An cafke dillalan miyagun kwayoyi 2 a Abuja, sun yi kashin sunki 165 na hodar Iblis

An cafke dillalan miyagun kwayoyi 2 a Abuja, sun yi kashin sunki 165 na hodar Iblis

  • Hukumar NDLEA ta yi ram da wasu mutum biyu da ake zargi da zama dillalan miyagun kwayoyi a filin jirgin sama na Abuja
  • Yayin da aka tistiye su, sun yi kashin sunki 165 na hodar Iblis wanda suka hadiya daga kasashe daban-daban da suka taho
  • A cewar daya daya cikinsu, za a biya shi dala dubu daya da yayi nasarar kai kwayoyin, yayin da dayan yace kudinsa ya narka ya siyo

Abuja - Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Elvis Uche Iro, mai shekaru 53 da kuma Uwaezuoke Ikenna Christian mai shekaru 42, wadanda rahotanni sun bayyana cewa sun yi kashin da hodar iblis 165.

Hukumar NDLEA ta ce ta kama su ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, Abuja.

Kara karanta wannan

Na yi mankas da kwayoyi kafin in zaneta: Matashin Bakano da ya halaka kakarsa, ya jefa gawarta a rijiya

An cafke dillalan miyagun kwayoyi 2 a Abuja, sun yi kashin sunki 165 na hodar Iblis
An cafke dillalan miyagun kwayoyi 2 a Abuja, sun yi kashin sunki 165 na hodar Iblis. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja cewa Elvis an kama ya shiga hannu a ranar Asabar 19 ga watan Maris, a lokacin da ya iso ta jirgin Ethiopian Airline daga Addis-Ababa bisa zarginsa da hadiye sunki 65 na hodar iblis mai nauyin kilogiram 1.376.

“Lokacin da aka yi hira da shi a karon farko, ya yi ikirarin cewa shi mai sana’ar adon cikin gida ne amma dole ne ya shiga harkar fataucin miyagun kwayoyi saboda yana bukatar kudi don fara sana’ar shayi, ya kula da iyalinsa da kuma adana sabon shagon da ya samu tare da kayayyakin labule da kayan masarufi a Legas.
"Ya ce da ya yi nasarar isar da kwayoyin, da an biya shi dala 1,000 a Abuja," in ji Babafemi.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ga masu sukar APC: Taron gangami ne a gabanmu, ba ta kowa muke ba

An ruwaito yadda wani fasinja Kirista da ke cikin jirgin, ya sha kwaya kwal 100 na hodar ibilis mai nauyin kilogiram 2.243.

Ikenna ya yi ikirarin cewa shi dan kasuwa ne shi mai sana’ar siyar da kayan sawan jarirai kafin ya shiga safarar miyagun kwayoyi.

A yayin da ake masa tambayoyi, ya ce ya je Addis Ababa ranar Alhamis, 17 ga watan Maris, domin sayan kwayoyin kan dala 10,000, ya kuma dawo ranar Asabar, 19 ga Maris, lokacin da aka kama shi.

Uwaezuoke ya ce ya sayar da filayensa a kauyensu kuma ya karbi lamuni daga abokansa domin ya samu kudin sayen kwayoyin.

Ya kuma yi ikirarin cewa dole ne ya shiga harkar kwaya don samun kudi don kasuwancinsa bayan da abokinsa da ke zaune a China ya yi masa zambar dala 15,000.

NDLEA ta kwace wiwi mai nauyin 374.397kg daga masu safara a jihar Kano

A wani labari na daban, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA), a jihar Kano ta bayyana yadda ta kama wiwi mai nauyin kilo 374.397, da wasu mutane 131, wadanda ake zargin su da safarar miyagun kwayoyi tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairu, 2022.

Kara karanta wannan

NDLEA ta kwace wiwi mai nauyin 374.397kg daga masu safara a jihar Kano

Kwamandan NDLEA na jihar, Abubakar Idris Ahmad, ya bayyana hakan ne a Kano yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba.

Ya ce, an damko wadanda ake zargin a wurare daban-daban a cikin jihar, bayan tsananta bincike da jami'an rundunar suka yi, inda ya kara da bayyana yadda wadanda ake zargin suka kunshi maza 125 da mata shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng