Yadda sojoji suka kwace iko a filin jirgin Kaduna daga harin da ‘yan ta’adda suka kai kan na’urori

Yadda sojoji suka kwace iko a filin jirgin Kaduna daga harin da ‘yan ta’adda suka kai kan na’urori

  • A jiya Asabar ne ‘yan ta’addan da suka kai dari biyu suka tsinkayi filin sauka da tashin jiragen sama na Kaduna
  • An gano cewa, miyagun sun zargi cewa sojoji sun kwashe musu shanunsu, lamarin da yasa suka sha alwashin hana ayyukan ranar
  • Sai dai, zakakuran sojojin Najeriya sun bude wa miyagun wuta inda suka kwace iko a filin sauka da tashin jiragen saman

Kaduna - A ranar Asabar din da ta gabata ne ‘yan ta’addan da yawansu ya kai 200 suka dire filin jirgin sama na Kaduna da ke karamar hukumar Igabi a Kaduna, inda suka dakile aiki tare da kashe jami’in tsaro daya na hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya.

Harin ya haifar da tashin hankali a filin jirgin, inda rahotanni suka ce an hana jirgin AZMAN da ke kan hanyar Legas ya tashi da karfe 12:30 na rana.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Hana Jirgin Sama Tashi a Kaduna, Sun Bindige Mutum Daya Har Lahira

Yadda sojoji suka kwace iko a filin jirgin Kaduna daga harin da ‘yan ta’adda suka kai kan na’urori
Yadda sojoji suka kwace iko a filin jirgin Kaduna daga harin da ‘yan ta’adda suka kai kan na’urori. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Majiyoyi a hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya sun shaidawa jaridar Sunday Punch cewa, ‘yan ta’addan sun kai hari a wurin da kayan aikin VHF a filin jirgin suke kuma sun kashe wani jami’in tsaro da ke gadin wurin.

Harin, an tattaro cewa, ya tilastawa mahukuntan filin tashi da saukar jiragen saman rufe harkokin na wani dan lokaci, yayin da sojoji ke fafatawa da wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya da ta sanar wa manema labarai, ta ce ‘yan ta’addan sun sha alwashin rufe tashar jirgin.

Majiyar ta ce, “Harin ‘yan ta’addan ya fara ne da misalin karfe 12 na safe (Asabar). Sai da tsakar dare suka fara kai hari filin jirgin. An ce ‘yan ta’addan sun yi zargin cewa jami’an soji sun kwashe shanunsu.
“Amma sojoji sun yi nasarar fatattakar su a tsakar daren kuma mun yi tunanin hakan ke nan. Hasalima ma’aikatan mu sun koma bakin aiki yau da safe kamar yadda suka saba. Sun yi aiki a kusa da titin jirgi na biyar har zuwa karfe 12 na dare.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan sanda sun karbe majalisar Cross River bayan tsige yan majalisa 20

“Bayan haka, babu jimawa, wasu ma’aikatan NAMA sun je duba wasu kayan aikinsu sai ‘yan bindigar suka bayyana suka fara harbi. Injiniyoyin NAMA sun yi tsere don kare kansu; ba su iya shiga motar da ta kai su wurin ba. Ana cikin haka ne aka harbi mai tsaron nasu a kai
"An garzaya da jami'an tsaron asibiti kuma an tabbatar da mutuwarsa."

Mukaddashin babban manajan hukumar kula da filayen jiragen sama na tarayyar Najeriya, Voke Ivbaze, yayin da take tabbatar da faruwar harin ga Sunday Punch, ta ce shiga tsakani da sojoji suka yi ne ya hana ‘yan fashin dakatar da ayyukan hukumar ta FAAN.

Da aka tambaye ta ko harin ya shafi ayyukan FAAN a filin jirgin, sai ta amsa da cewa, “A’a, ba duka ba. Da safe ne sojoji suka iya shiga tsakani.
"Don haka, bai shafi ayyukanmu ba kuma a zahiri jiragen biyu da ke kasa a lokacin, sun tashi daga bisani."

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamna El-Rufai ya sanya dokar hana fita a Jema'a da Kaura a jiharsa

A wata sanarwa da ta fitar a daren ranar Asabar, FAAN ta bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kai hari a titin Runway 05 na filin jirgin.

'Yan Bindiga Sun Hana Jirgin Sama Tashi a Kaduna, Sun Bindige Mutum Daya Har Lahira

A wani labari na daban, hankulan mutane a Kaduna ya tashi a yayin da yan bindiga suka kai hari filin tashin jiragen sama suka hana wani jirgi tashi daga filin, Nigerian Tribune ta rahoto.

Bincike ya nuna cewa jirgin yana shirin tashi ne zuwa Legas a ranar Asabar, a lokacin da bata garin suka kai kutsa titin jirgin hakan yasa ma'aikatan jirgin da fasinjoji suka tsere.

A cewar wata majiya da ta nemi a boye sunanta, yan bindigan sun harbi wani ma'aikacin hukumar kula da sararrin samaniyar Najeriya, NAMA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng