'Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Hana Jirgin Sama Tashi a Kaduna, Sun Bindige Mutum Daya Har Lahira

'Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Hana Jirgin Sama Tashi a Kaduna, Sun Bindige Mutum Daya Har Lahira

  • Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari filin tashin jiragen sama na kasa da kasa da ke Jihar Kaduna a ranar Asabar
  • Yayin harin, daya daga cikin yan bindigan ya harbe wani jamiin hukumar NAMA har lahira yayin da saura suka tarwatse
  • Daga bisani an tura dakarun sojojin Najeriya cikin motocci fiye da 10 inda suna can suna fafatawa da miyagun yan bindigan

Kaduna - Hankulan mutane a Kaduna ya tashi a yayin da yan bindiga suka kai hari filin tashin jiragen sama suka hana wani jirgi tashi daga filin, Nigerian Tribune ta rahoto.

Bincike ya nuna cewa jirgin yana shirin tashi ne zuwa Legas a ranar Asabar, a lokacin da bata garin suka kai kutsa titin jirgin hakan yasa ma'aikatan jirgin da fasinjoji suka tsere.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka kwace iko a filin jirgin Kaduna daga harin da ‘yan ta’adda suka kai kan na’urori

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Filin Tashin Jiragen Sama Na Kaduna, Sun Hana Jirgi Tashi
'Yan Bindiga Sun Kai Hari Filin Tashin Jiragen Sama Na Kaduna, Sun Hana Jirgi Tashi. Hoto: The Punch
Asali: UGC

'Yan bindigan sun harbi jami'in hukumar NAMA

A cewar wata majiya da ta nemi a boye sunanta, yan bindigan sun harbi wani ma'aikacin hukumar kula da sararrin samaniyar Najeriya, NAMA.

Duk da cewa babu cikakken bayani game da harbin ma'aikacin, an gano cewa yan bindigan sun harbe shi ne a titin tashin jirgin.

An rahoto cewa jirgin da aka shirya ya tashi misalin karfe 12.30 na ranar Asabar ya fasa tashin saboda yan bindigan.

An tura sojoji zuwa filin jirgin domin fatattakar yan bindigan

"A halin yanzu da muke magana, an tura sojoji wurin domin inganta tsaro, duk da cewa mafi yawancin ma'aikatan sun tsorata saboda kashe jami'in Nigerian Airspace Management Agency (NAMA), " a cewar majiyar.

A lokacin wallafa wannan rahoton, an tura motoccin sojoji fiye da 10 zuwa filin tashin jiragen domin inganta tsaro.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Sojoji da ke sintiri a Sambisa sun samo ragowar jirgin NAF da yayi hatsari a 2021

Kazalika, jami'an tsaro da wakilin Nigerian Tribune ya tuntuba ba su riga sun bada amsa ba kan lamarin.

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Hakazalika, Legit.ng Hausa ta samu ji ta bakin wani ma'aikaci a hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya, wanda ya nemi sa sakaya sunansa shima ya tabbatar mata da harin.

Ya ce yan bindigan sun yi yunkurin ratsowa filin tashi da saukan jiragen amma jami'an tsaro sun dakile harin.

Kara karanta wannan

Bayan zabtare albashin masu mukamai, hotunan shugaban kasar Ghana a Aso Rock sun bayyana

Ya kuma tabbatar da mutuwar wani injiniya da ke aiki a filin tashin jiragen da yan bindiga suka harba.

"Da gaske ne yan bindigan sun yi yunkurin shigo wa su kawo hari filin jirgin, jami'an tsaro sun taka musu birki. Sun bindige mutum daya ya mutu, injiniya da ya tafi duba lankarki na titin jirgin," a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164