Amurka Ta Bayyana Sunayen Ƴan Najeriya 6 Masu Taimakawa Ƙungiyar Boko Haram
- Gwamnatin kasar Amurka ta bayyana sunaye 6 na wasu ‘yan Najeriya a matsayin wadanda aka gano suna tamaka wa kungiyar Boko Haram
- Cikin mutanen da ka bayyana akwai Abudurrahman Ado Musa, Muhammad Ibrahim Isa, Bashir Ali Yusuf, Ibrahim Ali Alhassan, Surajo Abubakar Muhammad da Salihu Yusuf Adamu
- Kamar yadda bayanai suka nuna, an shigar da sunayen su cikin kundin masu taimaka wa ayyukan ta’addanci bisa umarnin shugaban kasar
Amurka - Gwamnatin kasar Amurka ta bayyana sunayen ‘yan Najeriya guda 6 masu taimaka wa kungiyar ta’addanci ta Boko Haram da ayyuka na musamman da kuma kudade, VOA ta ruwaito.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana yadda sashin kulawa da kadarorin ketare na Hukumar harkokin kudade na kasar Amurka, ta fitar da jerin sunayen.
A sanarwar da ta fitar ranar Juma’a, cikin wadanda sunayensu suka bayyana akwai Surajo Abubakar Muhammad, Abdurrahman Ado Musa, Ibrahim Ali Alhassan, Salihu Yusuf Adamu, Muhammad Ibrahim Isa da Bashir Ali Yusuf.
Kamar yadda sanarwar ta nuna bisa ruwayar VOA, wadanda sunayen nasu ya bayyana suna amfani da hanyoyi da dama wurin hidimta wa kungiyar ta fannoni na fasahohin zamani.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwar ta nuna yadda sunayen suka shiga kundin masu tallafa wa ayyukan ta’addanci, bisa umarnin shugaban kasar na 13224.
Kungiyar ta dinga tafka asarar rayuka a Najeriya
Sanarwar ta nuna cewa:
“Matakin da aka dauka yau ya biyo bayan hukuncin da kasar Daular Larabawa, UAE ta yanke, inda ta nuna su a matsayin masu taimaka wa ayyukan ta’addanci.”
Ranar 14 ga watan Nuwamban 2013, ma’aikatar harkokin kasashen waje ta kasar Amurka, ta ayyana kungiyar Boko Haram a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.
Kungiyar ce ke da alhakin kai hare-hare ga mutanen arewa da kuma arewa maso gabashin Najeriya da wasu yankuna na Kamaru, Chadi, Nijar da Tafkin Chadi, wadanda suka yi ajalin dubabbanin mutane tun daga 2009.
Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane, sun ƙona gidaje masu yawa
A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla fararen hula uku ne suka riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai hari a kauye da ke karamar hukumar Chibok a Jihar Borno da yammacin ranar Jumma'a.
Kungiyar yan ta'addan sun afka kauyen Kautikari da ke kusa da gari Chibok misalin karfe 4 na yamma, suna harbe-harbe ba kakkautawa kuma suka kona gidaje da dama a cewar majiyoyi na tsaro, Daily Trust ta ruwaito.
A cewar majiyar, maharan sun iso ne a cikin motocci guda biyar dauke da bindiga mai harbo jiragen yaki kuma suka shigo cikin sauki ba tare da an nemi taka musu birki ba.
Asali: Legit.ng