Yarjejeniyar takara: APC za ta shirya fitar da jerin sunayen hadin kai na taron gangami

Yarjejeniyar takara: APC za ta shirya fitar da jerin sunayen hadin kai na taron gangami

  • Jam’iyyar APC mai mulki na kokarin ganin cewa taronta na gangami na kasa bai rikide zuwa fagen fada ba
  • Gabanin taron, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce za a fitar da jerin sunayen hadin kai a ranar Juma’a 25 ga watan Maris
  • Ana sa ran cewa jerin sunayen za su kunshi sunayen ‘yan takarar da za su fito a matsayin sabbin mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar APC ta hanyar yarjewa

Abuja - Shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan jama’a na jam’iyyar APC mai mulki kuma gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule, ya ce a yau ne APC za ta shirya jerin sunayen hadin kan taron gangamin jam’iyyar na gobe Asabar.

Jaridar The Nation ta ce, Sule ya tabbatar da cewa tuni wasu shiyyoyin siyasar kasar nan suka amince da jerin sunayen da za a hada su a yau Juma'a.

Kara karanta wannan

Osinbajo: Duk Musulmin da ya zabi dan cocin RCCG munafikin Musulunci ne, MURIC

Taron gangamin APC: Jam'iyya na shirin fitar da jerin sunayen hadin kai
Da dumi-dumi: APC ta shirya fitar da jerin sunayen hadin kai gabanin taron gangamin | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Da yake jawabi a taron ganin babban taron gangamin da aka yi ranar Juma’a a Abuja, Sule ya kuma tabbatar da cewa tsarin yarjejeniyar ya kasance zabin farko na zaben sabbin shugabannin jam’iyyar.

Jaridar Punch ta ruwaito gwamnan na Nasarawa yana cewa:

"Daga abin da muke da shi a yankuna daban-daban, jerin hadin kai zai kasance a shirye a yau. Za a mika shi. Idan kuna magana akan yarjejeniya, dole ne ku sami jerin wadanda suka hada kai, saboda wannan shine gaba daya manufar yarjejeniya.
“Idan za ku yi yarjejeniya, za ku samu mutanen da suka amince, 'yan takaran da suka amince, da masu ruwa da tsaki da suka amince, da kuma mazabar da suka amince, kuma idan aka yi haka, za a karbi wannan sunan kai tsaye. Kuma wannan shine kawai ma'anar jerin hadin kai."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu ta dage zaman shari'a kan sauya shekar gwamna Ayade zuwa APC

Kudin Paris Club: Kotu ta yi watsi da wata kara da jihohi 36 suka shigar kan gwamnatin Buhari

A wani labarin, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da manyan lauyoyin gwamnatin jihohi 36 suka shigar kan gwamnatin tarayya.

A cikin karar, jihohin na kalubalantar shirin cire dala miliyan 418 daga asusun tarayya don biyan basussukan da wasu masu ba da shawara na jihohi da kananan hukumomi ke bin su dangane da kudaden Paris Club.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi watsi da karar ne a wani hukuncin da ya yanke a ranar Juma’a, yana mai cewa manyan lauyoyin ba su kawo isassun shaidun da za su ba su gamsar da kotu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.