Yanzu-yanzu: Kotu ta dage zaman shari'ar hukunci kan sauya shekar gwamna Ayade zuwa APC
- Yayinda ake sauraron hukuncin kotu kan Gwamnan jihar Cross Rivers a yau, Alkali ya dage zama
- Jam'iyyar PDP ta kai karar gwamna Ayade kotu bisa sauya shekar da yayi jam'iyyar APC
- Tuni da babbar kotun tarayya ta fitittiki gwamnan jihar Ebonyi kan sauya sheka APC daga PDP
Babban kotun tarayya dake Abuja ta dage zaman shari'a kan karar da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shigar na kwace kujerar Gwamnan jihar Cross River, Farfesa Ben Ayade da mataimakinsa, Ivara Esu.
Jam'iyyar hamayyar ta shigar da karar ne saboda sauya shekarsu zuwa jam'iyyar All Progressive Congress (APC).
An shirya zaman yanke hukunci kan lamarin yau amma Alkali Taiwo Taiwo ya dage zaman zuwa ranar 6 ga Afrilu, 2022, rahoton ChannelsTV.
Maye: Abu 5 da ya kamata ku sani game da Abdullahi Adamu, mutumin da Buhari ya zaba matsayin shugaban APC
Abinda ya fadawa yan majalisa ka iya fadawa kansa
Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta sallami wasu mambobin majalisar dokokin jihar Cross River su 20 a ranar Litinin, 21 ga watan Maris.
Kotu ta kwace kujerun su ne saboda sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki.
Kotun, a wani hukunci da mai shari’a Taiwo Taiwo ya yanke, ya riki cewa ya zama dole yan majalisar su sauka daga kujerunsu kasancewar sun yi watsi da jam’iyyar da ta dauki nauyin kawo su kan mulki.
Hukuncin ya biyo bayan wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/975/2021, da PDP ta shigar.
Asali: Legit.ng