Ikon Allah: Matar aure ta haifa ɗan jaki, ta bada labarin yadda tayi dakon cikin na shekara 2

Ikon Allah: Matar aure ta haifa ɗan jaki, ta bada labarin yadda tayi dakon cikin na shekara 2

  • Wata matar aure ta haifi dan jaki a garin Zariya bayan tan yi dakon cikin na tsawon shekaru biyu
  • Matar ta ce tsawon lokacin da ta kwashe da abun a cikinta ta kan kasance cikin hali na yau lafiya, gobe babu lafiya kuma liktoci basu ga komai ba da aka yi mata hoto
  • Ta ce da taimakon wata mata da ta bata ruwan addu'o'i da magungunan Musulunci sai gashi ta haifi dan jaki wanda suke zaton tura mata shi aka yi

Al’umman garin Zariya da ke jihar Kaduna sun shiga wani yanayi na dimuwa bayan an wayi gari wata mata ta haifi dan jaki.

A wata hira da wakilin Legit Hausa ya yi da ita, matar ta bayyana cewa tsawon shekaru biyu tana dauke da abun a cikin cikinta domin ta sha zuwa asibiti amma sai likitoci suce basu ga komai ba.

Kara karanta wannan

Maciya yake kirana: Mata ta kai kara gaban kotu, ta ce a raba ta da mijinta da ke gallaza mata

Ikon Allah: Matar aure ta haifa ɗan jaki, ta bada labarin yadda tayi dakon cikin na shekara 2
Ikon Allah: Matar aure ta haifa ɗan jaki, ta bada labarin yadda tayi dakon cikin na shekara 2 Hoto: The Cable
Asali: UGC

Ta ce ta kasance cikin wani mawuyacin hali tsawon lokacin domin ta kan kasance yau lafiya, gobe babu lafiya, sai a cikin haka Allah ya turo mata da wata baiwar Allah da ta zama sanadiyar warkewarta, sakamakon fitar mata da halittan da tayi daga cikinta.

Ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ni dai na godema Allah, wannan abu babu kokwanto, na dauke shi a matsayin kaddara, su kuma masu yi Allah ka shirye su. Shi dai wannan abu ina tare da shin a yi magani na asibiti, idan na je na yi hoto a ce ba’a ga komai ba.
“Cikin ikon Allah, Allah ya kawo wata baiwar Allah, tana ganina tace mun ga abun da yake tare da ni, nace mata toh shikenan. Kafin ma ta ce mun abun yana yi mun yawo, zance ma matan gida kun ga wannan abu yana yawo yana mun ciwo, toh da ni na ma dauke shi a ciwon sanyi, ashe ba ciwon sanyi bane, ajiya aka yi mun a cikin ciki. Aka hada ni da bakin aljani da jaki a cikina."

Kara karanta wannan

Nufin Allah ne: Duk da shafe shekaru biyu a aji daya a jami'arsu, yanzu ta gama da '1st Class'

Da aka tambaye ta game da tsawon lokacin da ta dauka da shi a cikinta, sai ta ce:

“Tun lokacin da na haifi waccan yarinyar bani da lafiya, ina ga yadda aka ajiye mun shi, tare da yarinyar aka ajiye mun shi. Toh da na haife ta, tun daga lokacin ban kara samun lafiya ba, yan cikina ya kumbura, gobe ya sake a haka nake, duk wanda ya ganni sai ya tausaya mun a kan wannan ciki, za a dauka haihuwa ne ashe cuta ne.”

Kan yadda rayuwarta ta kasance a lokacin da take dauke da cikin jakin da kuma alakarta da mutane, sai ta ce:

“Gaskiya ni ina zaune da mutane lafiya, kuma a rayuwata ina yawaita azumi da azkar, sallar dare, da addu’o’ duk ina yi. Toh shi wannan abun ya taso mun sai ya yi kamar zai kashe ni, haka yake yi mun, tafiya nan da can idan zan yi ta sai na huta. Amma jiya cikin ikon Allah da aka cire mani, ko ciwon kai ban kwana da shi ba.

Kara karanta wannan

Jibgegiyar Matata Tana Lakaɗa Min Duka Kuma Bata Nadama, Miji Ɗan Shekara 60 Ya Roƙi Kotu Ta Kashe Aurensa

“Su likitoci sun ce mun ruwa ne a cikin cikina."

Game da yadda aka cire mata shi, matar ta ce:

“Addu’o’i ta yi mani da Al-Qur’ani da magunguna na Islamic kemis. Tun bayan da aka cire mun kuma babu abun da ya same ni. Ina roko da al’umma da mu mata duk dan Adam ya ji tsoron Allah, ya kiyaye daukar alhakin mutum domin ta ce mun da abun ya mutu a cikina nima mutuwa zan yi.”

Wani makwabcinta kuma yayanta mai suna Danjuma Baban Abba ya tabbatar da al’amarin inda ya ce:

"Gaskiya abun da ta fada gaskiya ne, wannan baiwar Allah, Allah ya jarabceta da wata lalura kodayaushe cikinta a kumbure. Ta je asibiti aka ce mata ruwa ne a ciki da farko, sai aka yi kokarin cire wannan ruwa, daga baya dai wannan abu yana nan ya koma mata nan gobe ya koma mata gefe guda, daga karshe dai ta samu labarin wata baiwar Allah da ta zo daga Kano.

Kara karanta wannan

Diyar sanusi Lamido ta bayar da hakuri kan furucin da ta yi game da Larabawa

"Da wannan mata dai ta zo da yake Allah ya tsaga da rabonta, sai ta zo nan cikin gidan da ita wannan baiwar Allah Talatu take. Toh da ta kalleta sai tayi mata bayanin akwai wani abu a cikin cikinta. Toh ita a wannan lokacin abun ya bata tsoro. Sai tace idan ta yi tawakkali da Allah za ta bata ruwan rubutu da addu’o’I abun zai fita kuma cikin ikon Allah sai wannan halitta ya fita.
"A lokacin da wannan halitta ya fita, mu da kanmu hankalinmu ya yi mummunan tashi, ana cewa doki ne daga baya dai aka gane wannan halitta jaki ne. Kuma lallai an cire shi a jiya, wannan bayani da ta karanta maku haka yake, mu kanmu mun gani, ganau ne a zahiri haka abun yake.”

Maciya yake kirana: Mata ta kai kara gaban kotu, ta ce a raba ta mijinta da ke gallaza mata

Kara karanta wannan

Wani Da Ke Sallah a Masallacin Da Na Ke Limanci Ya Ɗirka Wa Matata Ciki, Liman Ya Faɗa Wa Kotu

A wani labarin, wata matar aure mai suna Misis Patience Ibrahim, a ranar Alhamis ta maka mijinta, Mista Talpha Atega, a gaban wata kotun gargadiya da ke Jikwoyi, Abuja, kan zargin kiranta da macijiya.

A korafinta, Patience ta fada ma kotun cewa Atega na yawan kiranta da ‘macijiya daga aljanun ruwa’, baya ga kin sauke hakokin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na mijinta, Vanguard ta rahoto.

Ta kuma roki kotu da kada ta mikawa mijin nata ragamar kula da da daya tilo da suka haifa, saboda tarbiyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng