Kuɗi ƙare magana: Bidiyon kek ɗin biki yana saukowa daga hadari yasa ƴan biki kurma ihu
- Wani kek din liyafar biki ya bayyana cike da salo inda ya sauko kasa da kansa a wani bidiyo da ya bayyana mai birgewa
- An ga kek din na saukowa daga wani abu mai kama da hadari, lamarin da ya bar 'yan biki cike da mamaki da sha'awa
- Abun ya matukar birgewa ta yadda ma'auratan ba su wahalar da kansu ba kuma kek ya same su har inda suke rawa
Wani bidiyo mai matukar birgewa ya nuna yadda kek din biki ya sauko daga hadari domin samun ma'auratan.
An ga angon da amaryar suna kwasar rawa kuma ba su wahalar da kansu ba wurin zuwa inda kek din yake sai dai ya sauko ya same su.
Ya kasance a sagale, yana rawa. Babu shakka kyakyawan kek din ya kayatar da liyafar.
Ko da kallon irin yadda aka tsara wurin liyafar, babu shakka za a gane cewa naira ta koka domin an kashe ta zuwa. An cika wurin da furanni tare da yanayi na hadari amma na masoya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kyakyawan bidiyon yasa jama'a masu tarin yawa sun sakankance cewa kudi ya yi, kuma alheri ne.
@gossipmilltv ne suka wallafa bidiyon a Instagram.
Masu amfani da soshiyal sun yi martani
Jama'a da yawa sun matukar nuna yadda kek din ya birgesu tare da yadda bikin ya tsaru. Ga wasu daga cikin martanin:
@honourablesteph ya ce: "Kek ya fado daga sama.. Wannan auren daga sama aka daura shi ba a Aba ba."
@wisdomcounsellin martani yayi da: "Darasin koyo: Idan ba ka iya biki mai tsada ba, ka yi liyafar da kake so domin sau daya ake yi a rayuwa, kada ka kashe kanka."
@naomikamara92 ta ce: "Mu ba mu da saurayin balle tsayayye... Ba za mu fara batun aure ba. Yanzu kuma batun yadda kek ke shigowa ake yi??? Ya Ubangiji, ga mu gare ka."
@fashion_magicblog ta yi tsokaci da: "Wani zai iya daukar wannan bidiyon ya kai wa masu tsarawa kan cewa yana so, amma sai ya fara tayi da kudin shi da basu taka kara sun karya ba."
Bidiyon mabaracin Legas dauke da bandiran kudi a jakunkuna ya janyo maganganu
A wani labari na daban, wani mabaraci ya jefa mutane da dama cikin tsananin mamaki bayan an kama shi da bandir-bandir na nairori a jakunkuna. An gano yadda kudaden ke da yawan gaske kuma sun kama tsakanin N1000 zuwa N100.
A halin yanzu bidiyon ne ke tashe a yanar gizo, wanda ke nuna makudan kudaden da mabaracin ya mallaka a jakunkunanshi.
An yi nasarar damke mabaracin, inda aka tilastashi ya zazzage dukkan jakunkunan da ya mallaka, inda aka ga kudi mai tarin yawa.
Asali: Legit.ng