EFCC ta saki tsohon gwamna bayan kwashe kwana 6 a hannunta, ta kwace fasfotinsa

EFCC ta saki tsohon gwamna bayan kwashe kwana 6 a hannunta, ta kwace fasfotinsa

  • Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa taannati, EFCC ta sako Willie Obiano, tsohon gwamnan Anambra
  • Bayan ya kwashe kwanaki shida a hannun hukumar, ya cike sharuddan belinta kuma ta kwace fasfotinsa
  • An kama gwamnan bayan awanni kadan da saukarsa kujerar gwamnan Anambra tare da mika mulki ga Soludo

A yammacin Laraba ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta saki tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, wanda yayi kwanaki shida a hannunta.

Wani jami’in hukumar, wanda ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin, ya bayyana cewa, “Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kwace fasfotin Obiano a matsayin wani bangare na sharuddan belinsa.”

EFCC ta saki tsohon gwamna bayan kwashe kwana 6 a hannunta, ta kwace fasfotinsa
EFCC ta saki tsohon gwamna bayan kwashe kwana 6 a hannunta, ta kwace fasfotinsa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren an kasa samun jin ta bakinsa har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: EFCC ta gano jami'in da ya yada bidiyon gwamna Obiano, za ta ladabtar dashi

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kama Obiano a ranar Alhamis da misalin karfe 8:30 na dare a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas, sa’o’i kadan bayan ya sauka daga kujerar gwamna tare da mika mulki ga sabon Gwamna, Farfesa Charles Soludo.

Daily Trust ta ruwaito cewa, rahotanni sun bayyana cewa yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Amurka lokacin da aka kama shi.

Daga nan aka mayar da shi hedikwatar hukumar, inda aka yi masa tambayoyi na kwanaki bisa zargin karkatar da kudin Sure-P na Naira biliyan 5, da kuri’un tsaro Naira biliyan 37, da fitar da tsabar kudi, da kuma wasu makuden kudaden kwangila.

Shugaban EFCC, Bawa, ya yi martani kan kamen tsohon gwamna, zargin cin zarafinsa a siyasance

Kara karanta wannan

Sunayen Gwamnoni 33 a Najeriya da hukumar EFCC ta kama bayan tube musu rigar kariya

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC), ta ce kamen Willie Obiano, tsohon gwamnan jihar Anambra tare da yi masa tambayoyi ba siyasa ba ne, Premium Times ta ruwaito

Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa, ya bayyana hakan a ranar Litinin da ta gabata a yayin da yake gabatar da amsar tambayoyi daga manema labarai a babban taron shekara-shekara na cibiyar yaki da cin hanci da rashawa a yammacin Afirka (NACIWA) karo na 5.

Bawa ya kara da cewa, hukumar ta bayar da belin Mista Obiano amma har yanzu tsohon gwamnan bai cika sharuddan belin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng