Gwamna Buni ga masu sukar APC: Taron gangami ne a gabanmu, ba ta kowa muke ba

Gwamna Buni ga masu sukar APC: Taron gangami ne a gabanmu, ba ta kowa muke ba

  • Jam'iyyar APC a makonnin da suka gabata ta kasance maudu'in tattaunawa a kafafen yada labarai bayan rahotannin da ke cewa jam'iyyae ba fama da rikicin cikin gida
  • Shugaban riko na jam’iyyar APC Mai Mala Buni ya gargadi masu yada labaran karya da nufin kawo cikas ga zaman lafiya a jam’iyyar
  • Buni ya kuma kara nanata cewa jam’iyyar tana nan a hade a matsayin tsintsiya daya, kuma ta mayar da hankali sosai wajen ganin an samu nasarar a taron gangaminta na kasa

Abuja - Shugaban kwamitin tsare-tsare na APC, Mai Mala Buni, ya ce jam’iyyarsu ta mayar da hankali kan taron gangami ne, kuma ba ta da lokacin sauraran kafafen yada labarai ko kuma masu wasa da hankalinta, inji rahoton PM News.

Buni wanda ya kasance maudu'in cece-kuce a makonnin da suka gabata biyo bayan rade-radin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kore shi daga mukaminsa, ya ci gaba da cewa jam’iyyar ba za ta lamunci duk wani nau’in raba hankali a cikinta ba.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC na kasa: Mika kujera wata shiyya ba ka'ida bane, Abdülaziz Yari

Gwamna Buni ga masu sukar APC
Gwamna Buni: Taron gangami ne a gabanmu, bamu da damu da sukar mai suka ba | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne ta wata sanarwa da kakakinsa, Mamman Mohammed ya rabawa manema labarai a ranar Laraba, 23 ga watan Maris.

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Muna ci gaba da kasancewa a inuwa daya, tare da mutunta shugabanmu da juna da kuma biyayya ga jam’iyyarmu.
“Mun dukufa wajen ganin mun cimma nasarar gudanar da taronmu na gangami na kasa mai zuwa, kuma ba za mu karkata daga wannan kyakkyawar manufa ta ciyar da jam’iyyar APC gaba ba."

Gwamnonin APC: Duk wanda Buhari ya zaba a taron gangamin shi za mu marawa baya

Gwamnonin jam’iyyar APC sun ce za su marawa duk wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya goyi baya a taron gangamin jam’iyyar na kasa da za a gudanar a ranar Asabar 26 ga watan Maris.

Shugaban kwamitin tsare-tsare na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya jagoranci gwamnonin zuwa wata ganawa da shugaba Buhari, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya shaida wa manema labarai bayan ganawar cewa za su goyi bayan duk wata hanya da za ta kai ga cimma matsaya wajen zaben shugabannin jam’iyyar.

Jaridar Daily Sun ta ce, a watan da ya gabata ne shugaba Buhari ya ce yana goyon bayan tsarin da aka amince da shi na zaben ‘yan takarar mukaman jam’iyyar na kasa.

Shirin 2023: Gwamnonin PDP daga jihohi 13 sun shiga ganawar sirri kan wasu batutuwa

A wani labarin, a yau ne kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP suka hadu domin tattaunawa a mahaifar gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu a Umuobiakwa, karamar hukumar Obingwa.

Rahoton da muke samu daga jaridar The Nation ya ce, gwamnan jihar Adamawa bai samu halarta ba, kana gwamnan Taraba Darius ya tura waikili, inda mataimakinsa Haruna Manu ya halarta.

Legit.ng Hausa ta lura cewa, rashin halartar gwamnan na da nasaba da taron da ke gudana a Abuja na ayyana aniyar tsayawa takarar Atiku Abubakar, kamar yadda muka ruwaito a baya.

Kara karanta wannan

Bikin sauya sheka: Tashin hankali yayin da jiga-jigan PDP 70 suka sauya sheka zuwa APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.