Jerin sunayen mutane 7 da majalisar dattawa ta tabbatar da su a kwamitin kula da harkokin kudi na CBN
- Majalisar dattawa ta tabbatar da sunayen mutane bakwai da shugaban kasa Buhari ya aike mata a matsayin mambobin kwamitin kula da harkokin kudi na babban bankin Najeriya
- Tabbatarwan ya biyo bayan nazari kan rahoton da kwamitin majalisar kan hada-hadar kudi ya gabatar
- A jawabinsa, shugaban kwamitin majalisar, Sanata Uba Sani ya ce wadanda aka tabbatar da nadin nasu sun cike abubuwan da ake bukata
Abuja - Majalisar dattawa, a ranar Laraba, 23 ga watan Maris, ta tabbatar da nadin mambobi bakwai na kwamitin kula da harkokin kudi na babban bankin Najeriya.
Hakan ya biyo bayan nazari kan rahoton da kwamitin majalisar kan harkokin bankuna, Inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi ya gabatar.
Shugaban kwamitin kuma sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Sanata Uba Sani ne ya gabatar da rahoton kamar yadda majalisar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta yi a shafinta na Twitter.
Shugaban kasa a 2023: Gwamna Tambuwal ya gana da IBB da Abdulsalami, ya bayyana shirin ‘yan takarar PDP
A wasikar da ya aike zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a ranar 23 ga watan Fabrairun 2022, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi bayanin cewa bukatar tabbatar da sabbin nadin ya yi daidai da sashi 12(4) na dokar babban bakin kasar, 2007.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sabbin nadin da majalisa ta tabbatar sune:
1. Farfesa Mohammed Adaya Salisu
2. Dr. Mo’Omamegbe
3. Farfesa Michael Obadan
4. Farfesa Festus Adeola Adenikinju
5. Farfesa Aliyu Sanusi Rafindadi
6. Dr. Robert Asogwa
7. Alhaji Aliyu Ahmed.
Sanata Uba Sani, a jawabinsa, ya ce wadanda aka nadan sun mallaki abun da ake bukata a bangaren karatu, ilimin fasaha da kuma gogewa don zama mambobin kwamitin na CBN.
Ya kuma bayyana cewa kwamitin majalisar dattawan bai samu kowani korafi a kan nadin nasu ba, inda ya kara da cewar hukumomin yan sanda, DSS da duk sun tantance su sannan sun mallaki takardar amincewa kotun da’ar ma’aikata.
Ya bayyana cewa daya daga cikin wadanda aka nada, Alhaji Aliyu Ahmed, ya kasance sakataren dindindin na ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa ta tarayya kuma zai yi aiki a matsayin wakilin ma’aikatar a kwamitin hada-hadar kudin.
Majalisar dattawa zata ɗaukaka kara kan hukuncin goge dokar zaɓe
A wani labari na daban, majalisar dattawan Najeriya ta cimma matsaya zata ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbbar Kotun tarayya dake zamanta a Umuahia, na goge sashi 84 (12) a kundin zabe 2022.
Hakan ya biyo bayan tafka muhawara kan kudiri mai taken, "Bukatar gaggawa na ɗaukaka kara kan hukuncin babar Kotun tarayya Umuahia a ƙara mai lamba FHC/UM/CS/26/2022 da ya shafi kundin zaɓe 2022."
Sanata George Sekibo mai wakiltar jihar Ribas ta gabas ne ya ɗauki nauyin kudirin, kuma ya samu mara bayan Sanatoci 80, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Asali: Legit.ng