Shirin 2023: Gwamnonin PDP daga jihohi 13 sun shiga ganawar sirri kan wasu batutuwa
- Yanzun nan muke samun labarin cewa, gwamnonin PDP sun shiga taron gaggawa game da wasu batutuwa
- Yanzu haka dai an ga gwamnoni kusan 13 ne suke cikin taron, inda wasu gwamnoni basu samu halarta ba
- Ana kyautata zaton gwamnonin za su tattauna kan batutuwan da suka shafi shiyya ne a zaman nasu
Abia - A yau ne kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP suka hadu domin tattaunawa a mahaifar gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu a Umuobiakwa, karamar hukumar Obingwa.
Rahoton da muke samu daga jaridar The Nation ya ce, gwamnan jihar Adamawa bai samu halarta ba, kana gwamnan Taraba Darius ya tura waikili, inda mataimakinsa Haruna Manu ya halarta.
Legit.ng Hausa ta lura cewa, rashin halartar gwamnan na da nasaba da taron da ke gudana a Abuja na ayyana aniyar tsayawa takarar Atiku Abubakar, kamar yadda muka ruwaito a baya.
Sauran wadanda suka halarci taron a jihar Abuja sun hada da Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu); Nyesom Wike (Rivers); Ifeanyi Okowa (Delta) da Godwin Obaseki (Edo).
Hakazalika, akwai Aminu Tambuwal ( Sokoto); Seyi Makinde (Oyo); Douye Diri (Bayelsa); Emmanuel Udom (Akwa Ibom) da Samuel Ortom (Benue).
Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance da gwamnatin jihar ta Abia ta yi kan ziyarar gwamnonin, amma an tattaro cewa, batun shiyya na daya daga cikin manyan abubuwan da za su tattauna akai.
Gwamnonin, har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, suna cikin ganawar ta sirri.
Ana sa ran za su yi jawabi ga manema labarai a karshen taron nasu.
Jaridar Punch ta yada hotunan da ke nuna wasu gwamnonin yayin da suke shirin shiga taron na sirri a jihar ta Abia.
Kalli hotunan:
Gudun rikici, Shugaba Buhari zai gana da yan takarar kujerar shugaban APC
A wani labarin, domin tabbatar da ba'a samu matsala a taron gangamin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Shugaba Muhammadu Buhar zai gana da yan takarar yau.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) za ta zabi sabbin shugabanninta na kasa ranar Asabar a farfajiyar Eagles Square dake birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun gabata cewa Shugaba Buhari na goyon bayan Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan jihar Nasarawa.
Asali: Legit.ng