Da Dumi-Dumi: Majalisar dattawa zata ɗaukaka kara kan hukuncin goge dokar zaɓe
- Majalisar dattawan Najeriya ta cimma matsaya zata ɗaukaka ƙara kan hukuncin Kotu cewa AGF ya goge wani sashin kundin zaɓen 2022
- A nata ɓangaren, Majalisar wakilai ta ɗauki mataki uku, da ya haɗa da dakatar da AGF zartar da hukuncin, da kai ƙarar Alkali gaban NJC
- Sashin dai ya kunshi duk wani mai rike da mukamin gwamnati ya yi murabus kafin shiga takarar zabe
Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta cimma matsaya zata ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbbar Kotun tarayya dake zamanta a Umuahia, na goge sashi 84 (12) a kundin zabe 2022.
Hakan ya biyo bayan tafka muhawara kan kudiri mai taken, "Bukatar gaggawa na ɗaukaka kara kan hukuncin babar Kotun tarayya Umuahia a ƙara mai lamba FHC/UM/CS/26/2022 da ya shafi kundin zaɓe 2022."
Sanata George Sekibo mai wakiltar jihar Ribas ta gabas ne ya ɗauki nauyin kudirin, kuma ya samu mara bayan Sanatoci 80, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Da yake jagorantar mahawara kan kudirinsa, Sekibo, yace sabon kundin zaɓe 2022 da Majalisa ta amince da shi ya bi dukkan matakan da kundin mulkin ƙasa 1999 ya tanada.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sashin 84(12) na kundin zaben ya kunshi cewa Ministoci, shugabannin hukumomin gwamnati da sauran naɗe-naɗen siyasa su yi murabus kafin shiga zaɓen fidda gwani, babban gangami da sauran harkokin zaɓe.
Wane hukunci babbar Kotu ta yanke kan dokar?
Babbar Kotun tarayya dake Zamanta a Umuahia, a ranar Jumu'a ta soke sashin, inda ta kafa hujja da cewa ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Bisa haka, Kotun ta umarci Antoni Janar na ƙasa kuma Ministan Shari'a ya tafi kai tsaye ya goge sashi na 84 (12) daga cikin kundin zabe 2022.
Wane mataki majalisar wakilai zata ɗauka?
Hakanan kuma, Majalisar wakilai a ranar Laraba, tace zata bi sahun Sanatoci, ita ma zata ɗaukaka ƙara kan hukuncin Kotu.
Majalisar ta kuma umarci AGF ka da ya yi gaggawar aiwatar da umarnin Kotu, domin zata bi dukkan matakai wajen ɗaukaka ƙara da nufin jingine hukuncin.
Ta kuma cimma matsaya a zamanta cewa zata kai korafin Alkalin Kotun da ya yanke hukuncin gaban majalisar alƙalai ta ƙasa (NJC) bisa shiga aikin ɓangaren masu dokoki.
Hakan ya biyo bayan kudirin da Mamban majalisar, Sada Soli ya gabatar, wanda ya kira hukuncin da cin mutuncin Majalisa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto
A wani labarin kuma Maraba da Ramadan: Gwamnatin Ganduje ta yi gyara a Kalandar makarantun Kano saboda zuwan Azumi
Yayin da Musulmai ke ta shirin tarban babban bako, gwamnatin Kano ta yi wani muhimmin gyara a Kalandar makarantun Firamare.
Gwamnatin karkashin gwamna Ganduje ta ba da umarnin rufe Firamaren gwamnati da masu zaman kansu saboda Ramadan.
Asali: Legit.ng