Shirin 2023: Atiku ya ayyana kudurinsa na gaje kujerar Buhari a zaben 2023

Shirin 2023: Atiku ya ayyana kudurinsa na gaje kujerar Buhari a zaben 2023

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ayyana aniyarsa ta sayawa takarar shugaban kasa a hukumance
  • ya bayyana hakan ne a dakin babban taro dake Abuja a gaban masoya da magoya bayansa na jam'iyyar PDP
  • Taron dai ya samu halarcin manya da sauran jiga-jigan jam'iyyar adawa ta PDP a sassan Najeriya daban-daban

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023, The Guardian ta ruwaito.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, ya bayyana matakinsa nasa ne a babban dakin taron kasa da kasa da ke Abuja.

Atiku zai tsaya takara
Yanzu-Yanzu: Atiku ya ayyana kudurinsa na gaje kujerar Buhari a zaben 2023 | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Dan takarar shugaban kasa na PDP a 2019 ya sha kaye a zaben baya a hannun shugaba Muhammadu Buhari wanda ke kan karaga a mulkinsa na biyu.

Kara karanta wannan

Gudun rikici, Shugaba Buhari zai gana da yan takarar kujerar shugaban APC

Sanarwar da Atiku ya yi na neman shugabancin kasar a 2023 ya zama karo na shida da zai tsaya takarar kujerar shugaban kasa zuwa yanzu.

Wadanda suka ayyana tsayawa takara a PDP zuwa yanzu sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, mawallafin mujallar Ovation, Dele Momodu, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, Pius Ayim da sauransu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, magoya bayan Atiku sun mamaye babban dakin taron na Abuja, domin nuna goyon bayansu ga ayyana tsayawarsa takarar shugaban kasa a 2023 a hukumance.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci ayyanawar ta Atiku sun hada da mataimakin shugaban kasa Muhammad Namadi Sambo; Gwamnan jihar Adamawa Umaru Fintiri; Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, Cif Tom Ikimi da dai sauran jiga-jigan PDP.

Kara karanta wannan

Idan PDP ta ba dan kudu tikitin shugaban kasa, ba zamuyi nasara ba: Tambuwal

Sauran magoya bayan nasa da suka halarci bikin da ke ci gaba da gudana har yanzu sun hada da Sanata Dino Melaye, Ambasada Roland Omowa da Josephine Anenih.

Maganar gwamna Fintiri game da Atiku

A nasa jawabin, Gwamna Fintiri ya shaida wa jama’a cewa Atiku Abubakar ya cancanci mulkin Najeriya saboda kwarewarsa a iya wakilci, inda ya kara da cewa

“Watakila shi ne dan takarar shugaban kasa mafi kwarewa a halin yanzu ba a jam’iyyarmu ta PDP kadai, ba har ma a kasar baki daya.”

Ya ce rashin nasarar da Atiku ya yi a tsawon shekaru, watakila akwai wata manufa game da hakan.

Gudun rikici, Shugaba Buhari zai gana da yan takarar kujerar shugaban APC

A wani labarin, domin tabbatar da ba'a samu matsala a taron gangamin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Shugaba Muhammadu Buhar zai gana da yan takarar yau.

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) za ta zabi sabbin shugabanninta na kasa ranar Asabar a farfajiyar Eagles Square dake birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

Rahotanni sun gabata cewa Shugaba Buhari na goyon bayan Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.