An gayyaci Shugaba Buhari taron bude sabon Masallacin Izalah da aka gina da kudin fatun Layya
- Kungiyar Izalah ta kammala ginin sabon Masallaci a unguwar Utako dake birnin tarayya Abuja
- Shugaba Muhammadu Buhari ne babban bako kuma Sarkin Musulmi ne Uban taro
- Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya yi kira ga mahalarta da su kasance a ciki da harabar masallacin kafin karfe sha biyu
Abuja - Kungiyar da'awa ta addinin Musulunci, Jama'atu Izalatul Bid'a Wa iqaamatus Sunna JIBWIS za ta bude sabon Masallacin da ta gina a birnin tarayya Abuja.
Za'a bude Masallacin ne ranar Juma'a, 25 ga Maris, 2022.
Shugaba Muhammadu Buhari ne aka gayyata a matsayin babban bako na musamman.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A jawabin da sakataren kungiyar na kasa, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya saki kuma Legit ta samu, ya sanar da Uban taro matsayin mai alfarma sarkin musulmi Alh. Abubakar Sa’ad Muhammad III.
Jerin sunayen mutane 7 da majalisar dattawa ta tabbatar da su a kwamitin kula da harkokin kudi na CBN
A cewar Izalah:
"Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala, Shugaban Majalisar Malamai sheikh Dr. Ibrahim Jalo Muhammad, da shugaban majalisar agaji Engr. Mustapha Sitti a madadin kungiyar Izala ta kasa, na farin cikin gayyatar al’ummar musulmi zuwa taron bude masallacin JIBWIS da ta gina a helkwatar kungiyar dake birnin Abuja.
Za’a kaddamar da taron bude masallacin ne ranar juma’a 22-Sha’aban-1443H/ 25-March-2022 a lokacin gudanar da sallar juma’a a harabar masallacin dake unguwar utako a cikin birnin Abuja.
Babban Bako na musamman: Mai girma shugaban kasar Naijeriya Alh. Muhammadu Buhari.
Uban taro mai alfarma sarkin musulmi Alh. Abubakar Sa’ad Muhammad III"
Jawabin ya kara da cewa sauran baki sun hada da manyan malamai, Sarakuna, Sanatoci, ‘Yan majalisu, Gwamnoni da sauran al’umma.
Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya yi kira ga mahalarta da su kasance a ciki da harabar masallacin kafin karfe sha biyu na rana 12:00pm, ma’ana kafin isowar babban bakon.
Kazalika Akwai gagarumin wa’azi a wannan dare, kuma ana saka ran dukkan Malamai da Alarammomi na kungiyar zasu halarta insha Allah.
Izalah ta gina katafaren Masallaci da kudin fatun layya a Abuja
JIBWIS za ta bude sabon Masallacin da ta gina a birnin tarayya Abuja ranar Juma'a.
Jibwis a jawabin da ta saki ranar Talata ta bayyana cewa an gina ne da kudaden fatun layya da mutane ke badawa fisabilillah.
Izalah ta bayyana hotunan Masalaccin dake unguwar Utako, kwaryar garin Abuja.
Asali: Legit.ng