Kano: Tankan Fetur Ta Yi Taho Mu Gamu Da Trela, An Rasa Rai
- Wata trela mallakar kamfanin gine-gine na Julius Berger ta afka wa wata tankar man fetur a Jihar Kano
- Bayan motoccin biyu sun yi karo, gobara ta tashi wacce ta yi sanadin rasuwar direban trelar bayan an ceto shi a sume
- Saminu Yusuf Abdullahi, kakakin hukumar kwana-kwana na Jihar Kano ya tabbatar da afkuwar hatsarrin ya kuma ce a mika gawar mamacin ga yan sanda
Kano - Mutum daya ya riga mu gidan gaskiya bayan wata trela mallakar kamfanin Julius Berger ta yi taho mu gamu da tankan man fetur mallakar kamfanin fetur na Mege a Chiromawa kan hanyar Zaria road a Kano.
Lamarin ya janyo gobara ta da kona motocci biyu inda wani direban kamfanin Julius Berger, mai suna Aminu Dakatsalle ya riga mu gidan gaskiya bayan an ceto shi a sume, Daily Trust ta ruwaito.
Hukumar Kwana-kwana ta Kano ta tabbatar da afkuwar hatsarin
Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana na Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar da afkuwar lamarin ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Abdullahi ya ce tankar man fetur din tana dauke da fetur kimanin lita 60,000 amma ta samu matsala a kan titin na Zaria road, Daily Trust ta rahoto.
Ya ce trelan mallakan kamfanin gine-gine na Julius Berger mai lamba ENG 879 XB ta fada wa tankar fetur din ne hakan yasa ta kama da wuta.
Ya kara da cewa abin da ya yi sanadin hatsarin shine kwace wa da motar ta yi wa marigayin kuma an mika gawarsa zuwa ga ofishin Garun Malam.
Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira
A wani labarin, mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.
An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.
Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.
Asali: Legit.ng