Nayi bacci da mazaje sama da 5000 - karuwa
An ce Rosemary Johns mai shekaru 65 a duniya ce karuwa da tafi kowa tsufa a kasar Nairobi.
Uwar yara 8 a wani labara da aka buga a sanannan jaridar Nairobi, Standard Media, ya bayyana yanda tayi bacci da mazaje sama da 5000 (kuma ana ci gaba da kirge), yanda duk ya fara, kalubalan da ta fuskanta farkon fara karuwancin ta, yanda ta taso da yayanta da sauransu.
An haifi Rosemary kuma ta taso a kasar Tanzania, amma a shekara ta 1984, ta samu kanta a ‘Hooker Avenue’ a kasar Nairobi, gurin da aka fi sani da tsohon sana’a ta: karuwanci.
“Nayi aure ina da shekaru 16, amma bayan dan wani lokaci, mijina ya fara sharemu bayan na haifi yara biyar,” mu tuna a yanzu uwar yara takwas ( biyu sun mutu da dadewa yayin da sauran sun girma a kasar Tanzania).
“Yaci ace ina da yara 10 in ba dan bari da nayi sau biyu ba,” Rosemary ta bayyana cewa ta rabu da mijinta ta zama yar’aiki a Musoma,Tanzania, kafin ta koma kasar Nairobi inda “na shiga karuwanci a hanyar Digo inda muke jiran abokanan sana’ar mu safe da rana . Ta bayyana cewa tana iya amfani da mazaje 40 a” ranaku mai kyau”ko kuma mazaje biyar zuwa 10 a wasu ranakun.
KU KARANTA KUMA: An kama gauruwa a Lagas kan sanya mata karuwanci
Abubuwa da dama sun chanja a shekaru 30 da suka wuce yayin da “ a zamanin nan yara mata kanana suka shiga sana’ar, suna tuka motocin kansu ko kuma wasu sana’aoin. Amma wasu daga cikinsu nayi wa abokan sana’arsu maza sata. Suna tara dukiya da wuri kuma suna saka hannun jari, idan aka misalta da lokutan baya, ko ta fannin shigarsu ya sha bamban da na da. A da muna shiga mai kyau bama nuna tsiraicinmu don jawo hankalin mazaje.
Ta ce: “bakin cikin wuta da kiwon wadanan yaran ne ya tilasta ni komawa ruwa. Kafin wutar, ina siyan Kangas daga Mombasa na kuma siyar dasu a Nairobi. Na ari kudade da yawa a banki. Ina fatan cewa abubuwa zasu chanja wata rana. Kuma Allah zai shiga lamarin.
Asali: Legit.ng