Kaduna: Lauya Ya Yi Ƙarar Wani Mutum a Kotun Shari'a Saboda Ƙin Biyansa N100,000 Kuɗin Aikinsa

Kaduna: Lauya Ya Yi Ƙarar Wani Mutum a Kotun Shari'a Saboda Ƙin Biyansa N100,000 Kuɗin Aikinsa

  • Wani lauya ya yi wani Alhaji Yusha'u Abdullahi a kotun shari'a saboda kin biyansa 100,000 kudin aikin da ya yi masa
  • Wanda aka yi karar ya amsa wa kotu cewa tabbas sun amince zai biya kudin kuma an masa aikin amma yana neman rangwame ne
  • Alkalin kotun ya yanke hukuncin cewa dole Yusha'u ya biya kudin kafin ko ranar 4 ga watan Afrilu kuma babu rangwame tunda anyi yarjejeniya tunda farko

Kaduna - Wata kamfanin lauyoyi a Kaduna mai suna Moonlight Attorneys, a ranar Litinin, ta yi karar wani Yusha'u Abdullahi a kotun shari'a saboda kin biyan kudin N100,000 kudin aikin da suka masa.

Lauyan wanda ya shigar da karar, Atiku Abdulra'uf, ya bayyana cewa wanda aka yi karar ya nemi wanda ya shigar da karar ya yi masa aiki, kuma suka amince zai biya adadin a matsayin kudin aiki, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Alkali ya iza keyar magidancin Bakano gidan yarin kan satar Maggi

Kaduna: Lauya Ya Yi Ƙarar Wani Mutum a Kotun Shari'a Saboda Ƙin Biyansa N100,000 Kuɗin Aikinsa
Lauya Ya Yi Ƙarar Wani Mutum a Kotun Shari'a Saboda Ƙin Biyansa N100,000 Kuɗin Aikinsa a Kaduna. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa bayan an kammala aikin, wanda aka yi karar ya ki biyan kudin duk da yarjejeniya da suka yi, hakan yasa wanda ya shigar da karar ya taho kotu don a bi masa hakkinsa.

"Muna son kotun nan ta taimaka ta karbo mana N100,000 a matsayin kudin aiki daga Alhaji Yusha'u," In ji shi.

Wanda aka yi karar ya ce rangwame ya ke nema a kan kudin

A bangarensa, wanda aka yi karar ya ce ya san da batun kudin, amma yana bukatar a yi masa rangwame domin ya samu ikon biyan kudin a kan lokaci.

Alkalin kotu ya ce sai ya biya N100,000 tunda haka suka yi yarjejeniya

Amma, Alkalin kotun, Malam Nuhu Falalu, ya ki amincewa da rokon neman rangwamen da Yusha'u ya yi.

Kara karanta wannan

Babban Magana: 'Yan Sanda Sun Cafke 'Aljani' Da Ya Yi Yunƙurin Yin Damfarar N2.2m a Borno

Ya kara da cewa tunda wanda aka yi karar ya amince da cewa ana binsa kudin aiki N100,000, ya zama dole ya biya wannan kudin ranar 5 ga watan Afrilu ko kafin ranar.

Ya bada umurnin cewa a tsare wanda aka yi karar a kotu har sai amintaccen wanda zai iya karbarsa beli ya zo.

Wani Da Ke Sallah a Masallacin Da Na Ke Limanci Ya Ɗirka Wa Matata Ciki, Liman Ya Faɗa Wa Kotu

A wani labarin, Alhaji Lukman Shittu, wani malamin addinin musulunci a Oyo ya yi zargin cewa wani daga cikin wadanda suke sallah a masallacinsa ya ɗirka wa matarsa ciki, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan zargin ne yayin da ya ke bayani ga kotun kwastamare Grade A da ke zamanta a Mapo, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Shittu, wanda matarsa ta yi kararsa na neman saki, ya shaida wa kotun cewa matarsa tana bin mazaje kuma ta haifi ƴaƴa uku da bai da tabbas nasa ne, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

An Gurfanar Da Makanike a Kotu Saboda Sayar Da Motar Kwastomansa a Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164