Da dumi-dumi: Tsaro ya tabarbare a Imo, Buhari ya ce a tura karin jami'ai da makamai

Da dumi-dumi: Tsaro ya tabarbare a Imo, Buhari ya ce a tura karin jami'ai da makamai

  • Shugaba Buhari na Najeriya ya bayyana bacin ransa da yadda ake ci gaba da samun matsalolin da suka shafi tsaro a Kudu
  • Ya amince a kara tura jami'ai zuwa jihar Imo domin a fatattaki duk wasu masu tada zaune tsaye a jihar da kewaye
  • Hakazalika, ya amince da kai karin makamai da alburusai jihar, inda yace ya yi Allah wadai da barnar da ake aikatawa

Abuja - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da tura karin jami’an tsaro da makamai da alburusai don magance matsalar tsaro a jihar Imo.

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ne ya sanar da hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ganawa da shugaban kasar a fadarsa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

Uzodinma ya gana da Buhari, an biya masa bukatarsa
Da dumi-dumi: Tsaro ya tabarbare a Imo, Buhari ya ce a tura karin jami'an da makamai | Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

Shugaba Buhari dai ya gayyaci gwamnan ne zuwa fadarsa don tattauna kan harkokin tsaro a jiharsa.

Ya bayyana damuwarsa kan matsalar tsaro a yankin Kudu maso Gabashin kasar nan, sannan ya yi Allah wadai da harin da aka kai gidan Farfesa George Obiozor, shugaban kungiyar koli ta al'adun kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Uzodinma, yayin da yake magana kan ganawar tasa da shugaban kasa, ya ce an biya dukkan bukatunsa na magance matsalolin tsaron jiharsa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Buhari ya aikawa Gwamna, Minista da Hadiminsa gayyata, ya na nemansu yau a ofishinsa

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sammaci ga gwamnan jihar Imo, Ministan harkar wutar lantarki da mai ba shi shawara kan tattali.

Garba Shehu ya fitar da sanarwa a ranar Litinin, 21 ga watan Maris 2022 yana cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya bukaci ganin wadannan mutane.

Kara karanta wannan

Buhari ya aikawa Gwamna, Minista da Hadiminsa gayyata, ya na nemansu yau a ofishinsa

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce Muhammadu Buhari zai yi zama da Gwamna Hope Uzodinma, Injiniya Abubakar Aliyu da Farfesa Doyin Salami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.