Jerin abubuwa 8 da Hukumar Kwastam ta hana fitar da su zuwa kasashen waje
Hukumar kwastam ta Najeriya ta bayyana jerin abubuwa da kayayyaki da aka haramta fitar da su daga kasar.
Duk wani yunkuri na fitar da wadannan kayayyaki da aka ambata a fadin iyakokin kasar zai zama wanda baya bisa ka’ida kuma za a hukunta mutum a karkashin dokokin kasar da suka dace.
Legit Hausa ta tattaro wadannan kayayyaki da aka hana fitar da su kamar haka:
1. Masara
2. Katako
3. Danyen fata da duk fatan da ba a gama sarrafawa ba
4. Karafuna
5. Roba da ba a riga an sarrafa ba
6. Kayan tarihi
7. Namun daji masu hatsari da kayayyakinsu misali, Kada; Giwa, Kadangare, Mikiya, Biri, Kura, Zaki da dai sauransu
8. Duk kayan da aka shigo da su
Kwastam Ta Kama Motar Dangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250
A wani labarin kuma, Kwantrolla Janar na Kwastam, Team A Unit, Mohammed Yusuf, ya ce jami'an hukumar sun kwace wata motar babban Dangote makare da buhun shinkafa na kasar waje 250 da aka haramta shigo da su.
Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Ikeja, Legas, yayin taron manema labarai inda ya bada jawabin ayyukan da suka yi cikin makonni hudu a sassa daban-daban, The Punch ta ruwaito.
Ya bayyana cewa a cikin kayan da aka kwace akwai kwantena ta katako mai tsawon kafa 20; buhunan shinkafa masu nauyin 50kg guda 1000; taya na gwanjo guda 3,143; kunshin tufafin gwanjo 320; Buhun fatar jaki 44 da ganyen wiwi kilogiram 137.3.
Asali: Legit.ng