Ziyara: Shugaba Buhari zai dira jihar Legas, zai kaddamar da ayyuka, zai duba wasu

Ziyara: Shugaba Buhari zai dira jihar Legas, zai kaddamar da ayyuka, zai duba wasu

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki jihar Legas, inda zai kaddamar da wasu ayyuka
  • Hakazalika, shugaban zai duba wasu ayyukan da ake yi a jihar, inda zai duba matsayin ayyukan zuwa yanzu
  • Tafiyar shugaban ita ce ta farko kenan tun dawowarsa daga birnin Landan a makon da ya gabata

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Legas, inda zai duba tare da kaddamar da wasu ayyuka da ake yi a jihar.

A wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya fitar ta shafukansa na Facebook da Twitter, ya yada hotunan ayyukan da shugaban zai duba tare da kaddamarwa.

Sanarwar ta ce, shugaban zai kai ziyarar ta aiki ne a gobe Talata 22 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Buhari ya aikawa Gwamna, Minista da Hadiminsa gayyata, ya na nemansu yau a ofishinsa

Shugaba Buhari zai tafi Legas
Ziyara: Shugaba Buhari zai dira jihar Legas, zai kaddamar da ayyuka, zai duba wasu | Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Wani yankin sanarwar ya bayyana cewa Buhari zai duba ayyukan da ake yi a wata tashar jirgin ruwa da ake yi a jihar ta Legas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ahmad ya ce:

"A gobe ne shugaba Buhari zai kai ziyarar aiki Legas domin duba aikin da ake yi a tashar jirgin ruwan Lekki Deep Sea. Idan aka kammala aikin tashar ruwan tekun mai fa'idoji da yawa, za ta kasance tashar ruwa mafi zurfi a Najeriya kuma ana hasashen za ta kasance daya daga cikin tashoshin jiragen ruwa na zamani a yammacin Afirka."
"Matsayin Kammala ginin na @LekkiPort, ya zuwa ranar 27 ga Fabrairu, 2022, matsayin aikin ya kai 84.94%. A gobe ne shugaba MBuhari zai zagaya wurin a ziyarar aiki a jihar Legas."

Kaddamar da sabuwar tasha

Hakazalika, ya kuma ce, shugaban zai kaddamar da wata tasha da gwamnati ta gina tashar jirgin sama na Murtala Muhammed da ke a birnin na Legas.

Kara karanta wannan

Bode George: Zan tattara na koma Ghana sannan na dunga kallo daga nesa idan Tinubu ya zama shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta rahoto Ahmad na cewa:

"A gobe ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabuwar tasha a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas domin amfanin jama’a."

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga Landan bayan shafe kwanaki ana duba lafiyarsa

A makon jiya, mun samu labarin cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dura babban birnin tarayya Abuja, bayan shafe kwanaki da yawa a kasar Burtaniya.

Rahotanni daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa, shugaban ya tafi Landan kwanakin baya domin a duba lafiyarsa.

Daily Trust ta ce ta samo daga NAN cewa jirgin shugaban kasan ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne da misalin karfe 7.09 na dare.

s

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.