Karin bayani: Gwamna El-Rufai ya sanya dokar hana fita a Jema'a da Kaura a jiharsa
- Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita a wasu kananan hukumomin jihar guda biyu
- Wannan na zuwa ne yayin da lamurran tsaro ke kara zama barazana a yankunan da gwamnati ta ambata
- Gwamnati ta ce an sanya dokar ne a yau, kuma za ta fara aiki nan take domin shawo kan lamurra a yankin
Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita hana fita a kananan hukumomin Jema’a da Kaura biyo bayan samun bayanai na shawari daga hukumomin tsaro na jihar.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta shafinta na Twitter.
Sanarwar ta ce:
"Biyo bayan shawarwarin hukumomin tsaro, KDSG ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jema’a da Kaura tare da fara aiki nan take. Hakan na nufin taimakawa jami’an tsaro wajen daidaita al’amura a yankunan, da ceton rayuka da dukiyoyi da kuma ba da damar maido da doka da oda."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnatin jihar ta kuma bukaci daukacin mazauna yankunan da abin ya shafa da su bi umarnin hukumomi har sai an samu zaman lafiya a yankunan.
Idan baku manta ba, a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris, an kashe mutane akalla 15 a wani hari da wasu da ake zargin Fulani ne suka kai a Kagoro.
CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro
A wani labarin, kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta yi kira ga gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya ajiye girman kai sannan ya yarda cewa ya gaza magance kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ta’addanci da ke gudana a jihar, Daily Trust ta rahoto.
Shugaban CAN reshen jihar Kaduna, Reverend John Joseph Hayab, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, 21 ga watan Maris, inda ya fadama El-Rufai da tawagarsa da su mayar da hankali kan yakin da ceto jihar domin a tuna da shi a alkhairi bayan ya bar mulki.
Jawabin CAN na zuwa ne a daidai lokacin da aka karya doka da oda a yankin kudancin jihar.
Asali: Legit.ng