Diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da angonta Muhammad Turad sun samu 'karuwar da namiji
- Allah ya azurta diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da angonta Muhammad Turad da samun karuwar da namiji
- Hanan ta haifi santalelen dan nata ne a kasar Turkiyya a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris
- An sakawa sabon jinjirin suna Muhammad Zayd kamar yadda mahaifinsa ya bayyana
Diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan tare da mijinta Muhammad Turad Sha’aban, sun samu karuwar da namiji a kasar Turkiyya.
Wata majiya ta kusa da iyalan ta sanar da cewa an haifin dan ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris, Solacebase ta rahoto.
An kuma tattaro cewa daga uwar har dan suna nan cikin koshin lafiya.
Hakazalika shafin Instagram mai suna mr_mrs_arewa ya nakalto cewa Muhammad Turad ya sanar da labarin samun karuwar tasu a shafinsa, inda ya bayyana cewa sun sanya wa yaron suna Muhammad Zayd.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Turad ya rubuta a shafin nasa:
“Allah ya azurta ni da matata da haihuwar da namiji! Alhamdulillah.
“Mun saka masa suna Muhammad Zayd (Hibbu Rasulallah)."
Idan za ku tuna, Hanan ta auri sahibin nata ne a watan Satumban 2020, a wani gagarumin shagali da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ke ce addu'a ta da aka karba: Hanan Buhari da Muhammad Turad sun shekara 1 da aure
A baya mun kawo cewa diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Hanan Buhari da mijin ta, Muhammad Turad Sha'aban sun yi murnar cikarsu shekara daya cif da aure a ranar Asabar, 4 ga watan Satumba, 2021.
Hazikar mai daukar hoton tare da mijinta sun garzaya shafukansu na Instagram inda suka taya juna murnar cika shekara 1 da aure.
"Ke ce addu'a ta da aka ansa! Ina mana murnar zagoyar ranar auren mu" Mohammed ya wallafa yayin da ya hada da kyakyawan hotonsu tare.
Asali: Legit.ng