Zan yi murabus daga siyasa idan Buhari ya goyi bayan Tinubu: Mai Baiwa shugaban kasa shawara

Zan yi murabus daga siyasa idan Buhari ya goyi bayan Tinubu: Mai Baiwa shugaban kasa shawara

  • Hadimin Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai yi masa biyayya kan Tinubu ba
  • Babafemi Ojudu ya ce da ya goyi bayan Tinubu gwara ya bar siyasa ya koma aikin noma
  • Ojudu, wanda tsohon dan takarar kujerar gwamnan Ekiti ne yace Osinbajo zai goyi baya

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu, ya bayyana cewa gwanda ya koma gona da ya goyi bayan Bola Tinubu ya zama Shugaban kasa.

Ojudu ya bayyana hakan ne yayin hira da Chude Jideonwo, ranar Asabar.

A cewarsa, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya fi Bola Tinubu cancantar zama shugaban kasa.

Mai Baiwa shugaban kasa shawara
Zan yi murabus daga siyasa idan Buhari ya goyi bayan Tinubu: Mai Baiwa shugaban kasa shawara Hoto: Babafemi Ojudu
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayinda aka tambayesa shin idan shugaba Buhari ya goyi bayan Tinubu, shin zai bi sahu? Ojudu yace:

Kara karanta wannan

Bode George: Zan tattara na koma Ghana sannan na dunga kallo daga nesa idan Tinubu ya zama shugaban kasa

"Ko kadan. Na yi alkawari, sai dai in koma gona. Idan ban yarda da kai ba, ban zan taba aiki da kai ba."
"Muna sauraron Osinbajo ya fada mana idan zai yi takara. Ni dai ina son yayi, amma ba bayyana niyyarsa ba tukun, saboda haka zamu sauraresa, kuma akwai lokaci."
"Zai iya tsayawa a ko ina a duniya, yayi harka da matasa da tsaffi, ya san ilimin zamani kuma yana kawo mafita kan lamura."

Ku samar da sashin harkokin siyasa don tallata yan uwanku Musulmai, Tinubu ga shugabannin Musulunci

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya bukaci majalisar koli ta shari’a ta kasa da ta kafa wani sashi na harkokin siyasa domin wayar da kan mabiya addinin game da samar da shugaban kasa Musulmi a zaben 2023.

Da yake magana a taron kafin Ramadan na kungiyar ta SCSN, wanda aka gudanar a Osogbo, babban birnin jihar Osun, Tinubu ya ce Musulmai ba za su yarda a barsu a baya ba wajen shiga harkokin siyasar kasar.

Kara karanta wannan

Yadda titin Ohanmi a jihar Edo ya koma bayan wata guda kacal da kammalawa, BudgIT

Yayin da yake neman goyon bayan kungiyar don cimma kudirinsa na son zama shugaban kasa, Tinubu, wanda ya samu wakilcin Asiwaju Musulumi na jihohin Yarbawa, Edo da Delta, Cif Tunde Badmus ya jaddada bukatar ganin Musulmai sun shiga lamuran siyasar kasar kamar sauran kungiyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng