An daura: Sarkin Iwo ya angwance da Gimbiyar Kano, Firdausi bisa sadaki N1m
- Alkawari ya cika, an daura auren Sarkin Iwo na jihar Osun da gimbiya Firdausi Abdullahi Bayero
- An daura auren a gidan Madakin Kano bisa sadaki milyan daya
- Sarkin da kansa bai halarci daurin auren ba amma ya tura wakilan da zasu karba masa auren
Kano - Sarkin Iwo, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi (Telu 1), ya angwance da Firdaus Abdullahi, wacce jika ce ga marigayi mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.
An daura auren a gidan Madakin Kano, rahoton Daily Trust.
Daga cikin wadanda suka halarci bikin akwai mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu; Sarkin Yarbawan Kano, da Sarkin Yarbawan Zazzau, dss.
Wakilan Ango sun baiwa walliyin Amarya kudin sadaki milyan daya a gaban Madakin Kano, Yusuf Ibrahim Cigari.
Amaryar diya ce marigayi Madakin Kano, Alhaji Abdullahi Sarki Sani Yola.
Ta yi karatun difloma a harkar girke-girke a makarantar Kano Poly.
Ta taba aure a baya amma mijinta ya rasu.
Wakilin Ango, Babalaji of Iwo land, Barrister Ismail Oteyeku ya bayyana cewa cike suke da farin cikin bisa wannan aure.
Yace:
"Mun samu kyakkyawan tarba a nan. Ni ba bakin Kano bane saboda a Kano ajka haifeni. Saboda haka gda nazo."
"Saboda haka, Firdaus diyata ce."
Babban yayan amarya, Farouq Abdullahi Sarki Yola, yace Firdaus na da halaye na kwarai kuuma a gidan Sarkin Kano ta girma.
Yace:
"Muna matukar farin ciki da wannan aure. Kasan shi aure na iya kai mutum ko ina a duniya."
Bayan rabuwa da matarsa yar kasar Jamaica a shekarar 2019, Oluwo of Iwo ya gamu da sabuwar soyayya a kasar Kano.
Sarkin kasar Iwo ta jihar Osun, Adewale Akanbi (Telu 1), na gab da angwancewa da yar Sarki, Firdauz Abdullahi a jihar Kano.
An shirya auren ranar 19 ga Maris, 2022, a gidan Madakin Kano
Oba Adewale ya shahara da yaki da masu ikirarin addinin gargajiya a kasar Yarbawa.
A jawaban da yayi lokaci bayan lokaci, ya jaddada cewa Allah daya yake bautawa kuma bai bautawa gumaka kamar yadda al'ada ta bukata.
Hakazalika Sarkin na fito-na-fito da yan damfara yahoo-yahoo masu asiri don samun kudi.
Asali: Legit.ng