Ana hana Hausa/Fulani ganin Likitia a asibitin jami'ar Jos saboda sunce su yan jihar Plateau ne
Ana hana al'ummar Hausa/Fulani ganin Likitia a asibitin koyarwan jami'ar Jos saboda suna ikirarin cewa sun yan asalin jihar Plateau ne, sannan a tilastasu canza sunan jihohinsu.
Mutane sun dade sun korafin wannan abu dake gudana a asibiti JUTH gabanin bayyanar bidiyo dake nuna wata ma'aikaciyar asibitin tana tabbatar da hakan.
Asibitin JUTH dai ta gwamnatin tarayya ce ba ta jihar ba.
Daily Trust ta ruwaito cewa ta samu ji daga bakin wasu marasa lafiya da suka fuskanci wannan lamari yayinda suka je rijista.
Idan mutum yaje rijista, ana bashi fam ya cika inda zai rubuta sunansa, kabilarsa, jiharsa na asali da karamar hukumarsa.
Amma idan Hausa/Fulani Musulmai suka rubuta su yan asalin Plateau ne, sai ace musu su canza saboda babu Hausa/Fulani a tarihin jihar.
Idan mutum yaki bin yadda sukace, ba zai ga Likita ba.
Hakan ya tilasta wasu canza asalinsu zuwa Kano, Bauchi ko wata jihar Arewa.
A bidiyon, an ji ma'aikciyar na cewa:
"Jiharka ta asali daban take da jihar da kake zama. Misali, ni yar Ogbomosho a jihar Oyo ce, kuma kakkani na a Filato aka haifesu, shin zan ce ni yar Filato ce? A'a, da jihar Oyo zan yi amfani."
"Dalili shine idan muka fara rubuta bayanin cikin komfuta, kuma mutum Hausa/Fulani yace shi dan Filato ne kuma dan Jos ta Arewa, komfutar zata mutu."
"A na'urar, kabilu hudu kadai ke Jos ta Arewa; Jarawa, Naraguta, Buji da Berom.
Domin tabbatar da gaskiyar wannan zargi da ake yiwa asibitin, wani wakilin jaridar Daily Trust yayi basaja ya shiga asibitin matsayin mara lafiya.
Bayan karban Fam, jami'in asibiti ta tambayesa:
"Kai ba dan Filato bane. Kai dan Bauchi, Kano, Kaduna ko Sokoto ne ko?"
Sai ta sake tambayara mahaifinsa dan wani gari ne, yace mata Jos, Plateau. Sai ta sake tambaya Kakansa dan wani gari ne yace Jos. Sai tace sam, karya yake.
Tace:
"Zan koreka idan baka fada min gaskiya ba. Ai mun fada muku tun kan mu fara."
Gabanin dan jaridan, an kori wasu mata, kuma sai da suka canza jiharsu daga Filato suka mayar da shi Kano suka samu ganin Likita.
Jawaban wasu mara lafiya da abun ya shafa
Khadeeja Sani ta bayyanawa Legit Hausa cewa:
"Wlh watarana na raka baban mu asibiti Muna bada details dinshi na sawa a file.suka ce state of origin muka ce jos.suka ce baza su cika ce ba hausa tribe a plateau .daga qarshe dai muka ce su saka kano saboda mu samu muga likita."
Hajiya Rabi Hassan, ta bayyanawa Daily Trust yadda aka tilasta mata canza sunan jiharta lokacin rijista.
Tace:
"Akwai lokacin da na samu matsala da kafa ta. Sai na je asibiti, aka bani Fam in cika don ganin Likita."
"Da na rubuta ni yar Jos ce. An tilasta ni canzawa. Sai na fadawa ma'aikatan su canza min kawai saboda ta lafiyata nike.'
"Ba zan taba mantawa da wannan abu ba."
Aisha Ibrahim, tace:
"Yayinda suka kira lambata kuma na mika Fam din, daya daga cikin jami'an tace in koma in canza jihata da karamar hukumata kuma idan ban canza ba, ba zata saurareni ba. Sai da na canza."
Wata mara lafiyar Aisha Sani yar Febuna a Jos North ta bukaci wakilin Daily Trust ya tayata canzawa saboda ta samu ganin Likitta.
"Dan taya ni canza sunan asalin jihata da karamar hukuma. Sa in Kano. Ban san su koreni kamar yadda suka yiwa waccar matan. Ni Likita nike don gani."
Asibitin ta karyata labarin
Jami'ar hulda da jama'a na asibitin, Mrs Bridget Omini, ta ce abinda aka gani a bidiyon ba da sa hannun asibitin bane.
Tace:
"Ina mai bayyana cewa asibitin koyarwan jami'ar Jos mallakin gwamnatin tarayya ce dake da hakkin kula da kowa, ba tare da banbancin kabila ko addini ba."
"Muna kira ga jama'a suyi watsi da wannan bidiyo."
Asali: Legit.ng