Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kona Gidan Shugaban Kungiyar Ohanaeze Indigbo a Imo

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kona Gidan Shugaban Kungiyar Ohanaeze Indigbo a Imo

  • Wasu mahara da ake zargin yan bindiga ne sun kai hari gidan shugaban kungiyar kabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo a garinsu da ke jihar Imo
  • Yayin harin sun cinnawa gidan wuta ta hanyar jefa abubuwan fashewa a cikin gdan wadda haka yayi sanadin konewar gidan a Awo-Omanma
  • Rahotanni sun nuna cewa shugaban na Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor baya cikin gidan a lokacin da maharan suka taho suka kona gidan

Imo - Yan bindiga, a ranar Asabar sun kona gidan shugaban kungiyar Ohanaeze Indigbo, Farfesa George Obiozor, a Awo-Omanma a karamar hukumar Oru East ta Jihar Imo, The Punch ta rahoto.

The Punch ta tattaro cewa maharan sun isa gidan shugaban kungiyar na kabilar Igbo ne a motocci sannan suka jefa abubuwan fashewa cikin gidan.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ƴan Bindiga Sun Jefa 'Bam' Cikin Ofishin Ƴan Sanda, Sun Kashe Jami'ai 2, Sun Ƙona Motocci

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kona Gidan Shugaban Kungiyar Ohanaeze Indigbo Imo
'Yan Bindiga Sun Kona Gidan Shugaban Kungiyar Ohanaeze Indigbo Imo. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gano cewa Obiozor baya a gida a lokacin da aka kai harin.

Wata majiya ta ce:

"An kona gidan Farfesa George Obiozor a kauyensu. Na'urar dauka bidiyo na CCTV ta nadi yadda abin ya faru. Mun gode wa Allah Farfesan baya gida a lokacin da suka zo."

Kawo yanzu Obiozor bai ce komai ba game da binciken harin amma wani jagora na Ohanaeze Ndigbo, wanda ya nemi a boye sunansa ya ce ya kira Obiozor domin yi masa jaje bisa afkuwar lamarin.

Ya yi kira ga yan sanda su binciko wadanda suka kai harin suka kona gidan farfesan.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Imo, Micheal Abattam, bai riga ya bada bayani ba game da harin da ka kai wa gidan shugban na Igbo a garinsu.

Harin na gidan Obiozor a garinsu yana zuwa ne a daren da aka kai wani harin a ofishin yan sanda da ke Owerri ta Yammacin Jihar inda aka kone ofishin aka kuma kashe yan sanda biyu.

Kara karanta wannan

Anambra: Laifuka 3 da suka jawo aka kama tsohon gwamna Obinao garin tserewa Amurka

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164