Kungiyar Izala ta rabawa yan gudun Hijra da matsalar tsaro ta shafa a Neja kayayayyki

Kungiyar Izala ta rabawa yan gudun Hijra da matsalar tsaro ta shafa a Neja kayayayyki

  • Kungiyar Izalah ta kaiwa al'ummar jihar Neja da rikicin yan bindiga ya kora daga muhallansu dauki
  • Kungiyar da'awar Musuluncin ta raba buhuhunan shinkafa da sauran kayan hatsi don rabawa yan gudun Hijran
  • Jihar Neja na cikin jihohin da rikicin yan bindiga ya adda shekarun baya-bayan nan

Kungiyar da'awa ta addinin Musulunci, Jama'atu Izalatul Bid'a Wa iqaamatus Sunna JIBWIS ta kai dauki ga al'ummar jihar Neja da rikicin rashin tsaro ya kora daga muhallansu.

Kayan da aka raba sun hada da hatsi, tufafi da kayan shayi.

Izalah a jawabin da ta saki ta bayyana cewa shugabanninta na reshen Neja sun raba wadannan kayan abinci ne ga yan gudun Hijra daga kananan hukumomin jihar 13.

Kungiyar Izala
Kungiyar Izala ta rabawa yan gudun Hijra da matsalar tsaro ta shafa kayan abinci da tufafi Hoto: JIBWIS
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Jiragen Super Tucano sun yi lugude a maboyar ISWAP, Sani Shuwaram ya shura lahira, an nada sabon shugaba

Kungiyar tace "ta bada wannan tallafi ne ga yan gudun hijira dan rage masu radadin da suke fama dashi na rayuwa sakamakon fitin tinun yan ta'adda da ya raba su da garuruwan su."

JIBWIS ta bayyana hakan a shafinta na Facebook.

Jawabin yace:
"Shugaban kungiyar ta jahar Neja Alh Abdullahi Musa Mai Radiyo Shi ya jagoranci kaddamar da wannan gagarumin aiki
Kayayyakin sun haɗa da:
Shinkafa buhu 113
Semovita 100
Wake buhu 10
Masara buhu 5
Dawa buhu 1
Taliya Caton 105
Madara Caton 100
Sugar buhu 20
Indomi 210
Manja Jarka 20
Mangyada 50
Tabarma 250
Atamfa turmi 203
Sai kayan sawa na maza da mata"

Ƴan Bindiga Sun Ji Ba Daɗi A Hannun Jami'an Tsaro, Fiye Da 100 Sun Baƙunci Lahira

Jami'an tsaro na hadin gwiwa da suka hada da sojoji, yan sanda da yan sakai da ake kira vigilante a ranar Laraba da yamma sun dakile wata harin da yan bindiga suka so kai wa a Bangi, hedkwatar karamar hukumar Mariga, Jihar Neja.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga Landan bayan shafe kwanaki ana duba lafiyarsa

Mazauna garin sun bayyana cewa yan bindigan da suka nufo garin sun yi yunkurin kutsa wa hedkwatar ne misalin karfe 6 na yamma amma hadakar jami'an tsaron suka dakile harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng