Jami'an tsaro sun dakile wani yunkuri na kai hari birnin tarayya
- Yan sanda da sojoji sun dakile wani yunkuri na kai hari a yankin Dobi Kwalita da ke Gwagwalada
- Jami'an tsaron sun ceto wani bawan Allah da aka yi garkuwa da shi a yankin
- Mai magana da yawun yan sandan Abuja, DSP Josephine Adeh, ta tabbatar da haka
Abuja - Rundunar yan sandan birnin tarayya tare da hadin gwiwar sojoji sun dakile wani yunkuri na garkuwa da mutum sannan suka ceto wanda aka sace a yankin Dobi Kwalita da ke Gwagwalada.
Kakakin yan sandan birnin tarayya, DSP Josephine Adeh, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 17 ga watan Abuja, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ta ce an dakile harin sannan an ceto wanda lamarin ya ritsa da shi bayan wani rahoton sirri daga mazauna Dobi kwalita, rahoton Daily Post.
Adeh ta ce:
“Mazauna yankin sun zargi wani taron mutane da suka yi zargin masu garkuwa da mutane ne a yankin a ranar Talata.
“Biyo bayan rahoto, dabara da bayanan sirri na hedikwatar rundunar da ke yankin Gwagwalada sai ’yan sanda da taimakon sojoji suka shiga aiki.”
Ta ce an gaggauta tura jami’an yan sanda da yan banga zuwa wurin.
“A kokarin tserewa daga harin, ‘yan ta’addan sun fafata da dakarun inda su kuma suka yi nasara a kansu wajen dakile harin.
“A cikin haka, an ceto wani da aka yi garkuwa da shi, Sani Dauje, wani mazaunin Dobi Kwalita yayin da aka kama wani dan shekara 18 da ake zargin dan kungiyar ne.
"A halin yanzu, bindigu guda biyu masu lambobi: 56-128031015, suna hannun 'yan sanda sannan kuma wani mai lamba 1974HKOOO85 na a hannun sojoji, yayin da aka kwato harsasai 44.”
Neja: Ƴan Bindiga Sun Ji Ba Daɗi A Hannun Jami'an Tsaro, Fiye Da 100 Sun Baƙunci Lahira
A wani labarin, mun ji cewa jami'an tsaro na hadin gwiwa da suka hada da sojoji, yan sanda da yan sakai da ake kira vigilante a ranar Laraba da yamma sun dakile wata harin da yan bindiga suka so kai wa a Bangi, hedkwatar karamar hukumar Mariga, Jihar Neja.
Mazauna garin sun bayyana cewa yan bindigan da suka nufo garin sun yi yunkurin kutsa wa hedkwatar ne misalin karfe 6 na yamma amma hadakar jami'an tsaron suka dakile harin, rahoton Daily Trust.
Asali: Legit.ng