Karfin hali: Matar tsohon gwamna Obiano ta shararawa Bianca Ojukwu mari a wajen rantsar da Soludo

Karfin hali: Matar tsohon gwamna Obiano ta shararawa Bianca Ojukwu mari a wajen rantsar da Soludo

  • Wata babbar dirama mai mamaki ta kawo cikas na wani dan lokaci a wajen bikin rantsar da Farfesa Chukwuma Soludo a matsayin gwamnan jihar Anambra a ranar Alhamis
  • Ebelechukwu Obiano, matar tsohon gwamnan jihar, Willie Obiano, ta kaftawawa Bianca Ojukwu mari a bainar jama'a a wajen taron
  • Daga baya an tafi da Mrs Obiano kuma jim kadan bayan haka jami’an tsaro sun kwantar da tarzoma a wajen bikin rantsarwar

Anambra - An yi takaddama a ranar Alhamis yayin da aka rantsar da Farfesa Charles Soludo a matsayin gwamna inda matar Willie Obiano Ebelechukwu da Bianca Ojukwu suka kaure da fada, inji rahoton The Nation.

Matar Obiano ta gaurawa Bianca mari, inda ta zarge ta da cewa ba ta son mijinta ya zama Gwamna yayin da ta kira ta yar iska.

Kara karanta wannan

'Karin Bayan: Soludo Ya Yi Magana Kan Marin Da Matar Obiano Ta Yi Wa Bianca Ojukwu a Wurin Taron Rantsar Da Shi

Cikin fusata da bacin rai, Mrs Ojukwu ta mike ta mari matar Obiano, lamarin da ya kai ga fada tsakaninsu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rikici tsakanin matar tsohon gwamna
Da dumi-dumi: Matar tsohon gwamna Obiano ta shararawa Bianca Ojukwu mari a wajen rantsar da Soludo | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

PM News ta ruwaito cewa, wakilin NAN da ke wajen taron ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan da aka rantsar da Soludo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa manyan baki da suka hada da tsohon gwamna Obiano suna zaune a lokacin da Mrs Obiano ta shigo ta nufi layin gaba inda matar Dim Odumegwu Ojukwu ke zaune kana ta sharara mata mari a kunci.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa matakin ya ja hankalin jami’an tsaro da wasu mutane da suka janye Mrs Obiano daga jikin Bianca wadda ta rikice matuka da faruwar lamarin.

Daga baya an tafi da Mrs Obiano, kuma jim kadan, mijin nata ya bar wurin tun da lamarin ya faru bayan an rantsar da sabon gwamnan ne.

Kara karanta wannan

Kannywood: Ina fatan rabuwa da kowa lafiya nima na yi aure, Maryam Yahaya ta magantu

Sabanin rahotannin da suka gabata, jaridar The Nation ta kuma bayyana cewa Misis Ojukwu ce ta fara marin Mrs Obiano har lamarin ya kai ga fada.

Soludo Ya Yi Magana Kan Marin Da Matar Obiano Ta Yi Wa Bianca Ojukwu a Wurin Taron Rantsar Da Shi

Jim kadan bayan rikicin, Farfesa Charles Soludo, gwamnan Jihar Anambra ya nuna damuwarsa kan marin da matar gwamna mai barin gado, Elechekwu ta yi wa Bianca Ojukwu.

Ko da ya ke ya mayar da hankali wurin rattaba hannu kan takardun da alkalin alkalan jihar Mai Sharia Onochie Anyachebelu ya kawo masa.

A yayin da ya fara jawabinsa, ya ce:

"Wadanda suke son su tafi za su iya tafiya.
"Jihar Anambra da muke magana a kai wuri ne na bin doka da oda."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.