Aiki kai tsaye ga masu 1st Class: Majalisa ta tattauna kan daukar masu digiri aiki
- Majalisar wakilai ta caccaka tsinke kan batun samar wa masu digiri da sakamako mai kyau guraben aiki
- Wannan na zuwa ne yayin da kasar ke fuskantar asarar dalibai masu kwazo saboda rashin samun aikin yi
- Majalisar ta amince da batun da wani dan majalisa ya gabatar, ta ce a gaggauta bin hanyoyin da suka dace don tabbatar da hakan
FCT, Abuja - Majalisar wakilai na son a fara daukar aiki kai tsaye ga daliban da suka kammala digiri da sakamako mafi kyau daga cibiyoyin ilimi na Najeriya, rahoton Channels Tv.
Majalisar ta yi imanin cewa hakan zai zama hanyar karfafa kwarin gwiwa ga daliban Najeriya da kuma baiwa wadanda suka kammala karatu damar kara kaimi a karatunsu.
Yadda batun ya faro
Dan majalisar wakilai, Chinedu Martins, wanda ya gabatar da kudirin a ranar Laraba, ya ce hakan zai magance matsalolin ficewar daliban Najeriya masu hazaka daga kasar kamar yadda ake gani a yanzu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da yake gabatar da jawabinsa, Hon Martins ya jaddada cewa jami’o’in Najeriya na samar da daruruwan daliban da suka kammala karatun digiri da sakamako na matakin farko a duk shekara, inda ya kara da cewa:
“Kashi mai yawa daga cikinsu yana da wahala su samu ayyukan yi da ba da gudummawa ga gina kasa.”
Ya koka da cewa, rashin samun abin yi a kasar yasa da yawa daga cikin hazikan daliban Najeriya ke tsallakawa kasashen ketare domin samun na abin ka, inji The Guardian.
A cewarsa, bincike ya nuna cewa, Najeriya na asarar hazikin masu digiri da suka kammala da sakamako mai kyau, wadanda a cewarsa su ne za su iya kawo mafita ga abubuwa da dama suke addabar kasar nan ta fuskoki da dama.
Ya kara da cewa:
"Rahotanni sun nuna wajen neman shiga jami'o'i, dalibai suna la'akari da kasashe irin su Birtaniya, Amurka, Jamus, Faransa, Australia, China, Kanada saboda hakan kan kara musu damar samun aiki bayan kammala karatun."
Martanin Majalisa
Dan majalisar ya bayyana cewar ba da aikin kai tsaye ga daliban da suka kammala karatun digiri da maki mafi kyau zai zama wani abin zaburarwa ga dalibai su kara himma.
Bayan sauraron batunsa, majalisar ta amince da kudirin kuma ta bukaci ma’aikatar ilimi ta tarayya da ta hada kai da hukumomin gwamnati da abin ya shafa don tabbatar da samar da aikin yi ga daliban da suka kammala digiri da mafi kyawun sakamako a jami'o'in Najeriya.
'Yan majalisar sun kuma umarci kwamitocinta kan Ilimin Manyan Makarantu da Hidima, da Kwadago, Samar da Aiki da su yi aiki don tabbatar da bin batutuwan da aka cimma.
Yadda wasu ‘Yan Baiwa 3 daga Bauchi suka zo birnin ilmi, suka bar tarihi a ABU Zaria
A wani labarin, tun da aka kafa sashen ilmin jinya a jami’ar Ahmadu Bello watau ABU Zaria, mutane uku kacal aka iya samu suka fita da mafi kyawun digiri.
Abin ban mamaki da sha’awa, duka wadannan hazikan dalibai uku sun fito ne daga jiha guda - Bauchi. Jaridar The Nation ce ta fitar da wannan rahoto.
A shekarar 2017, Usman Usman Muhammad ya yi abin da ba a taba samun wanda ya yi ba tun shekarar 1997 da aka fara karantar da fannin jinya a ABU.
Asali: Legit.ng