Yanzu-Yanzu: Tinubu zai gana da Sanatocin jam'iyyar APC a yau dinnan
- A yau ne majalisar dattawa ta sanar da cewa, Tinubu na son ganawa da sanatocin jam'iyyar APC mai mulki
- Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa ne ya bayyana hakan a yayin zaman majalisa a yau Laraba
- Ya bayyana lokaci da wurin da sanatocin za su hadu da jagoran jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu
FCT, Abuja - 'Ya'yan jam’iyyar APC a majalisar dattawa za su gana da jagoran jam’iyyar APC mai mulki na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a yau Laraba, Leadership ta ruwaito.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan a cikin wata wasika da ya karanta yayin da aka fara zaman majalisar a safiyar Laraba.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi (Kebbi ta Arewa) ne ya sanya wa wasikar hannu.
A cewar Lawan:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Za a yi taro da 'yan majalisar dattawa na APC da mai girma Bola Ahmed Tinubu a yau 16 ga Maris, 2022."
Taron wanda aka shirya gudanarwa a dakin taron shugaban majalisar dattawa, an shirya yinsa ne da misalin karfe 2:30 na rana a harabar majalisar dokokin kasar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Tinubu dai dan takarar shugaban kasa ne a dandalin APC, inda kwanakin baya ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben 2023.
'Yan siyasar Najeriya na ci gaba da bayyana aniyarsu ta tsayawa takara.
Atiku Abubakar: Yadda Tinubu ya nemi ya zama mataimakina, amma na ce ban yarda ba
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bada labarin yadda ya yi watsi da tayin da Asiwaju Bola Tinubu ya kawo masa a zaben 2007.
Daily Trust ta ce Atiku Abubakar ya shaidawa Duniya cewa Bola Tinubu ya nemi su yi takara tare da shi a matsayin mai neman mataimakin shugaban Najeriya.
Wazirin na Adamawa bai yarda su hada tikiti da tsohon gwamnan na Legas ba. A karshe dai jam’iyyarsu ta AC ta sha kashi a hannun Ummaru ‘Yar’adua.
Asali: Legit.ng