Tserewa zai yi: NDLEA ta ki amincewa da bukatar belin Abba Kyari, an dage kara
- A yau ne aka ci gaba da zaman kotu a shari'ar da ake tsakanin Abba Kyari da abokan harkallarsa da hukumar NDLEA
- Ana zargin Kyari da tawagarsa ne da aikata mummunar harkallar safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa
- Ya zuwa yanzu, alkali ya zauna, ya kuma dage zaman kotun har zuwa 28 ga watan nan domin duba ba da belin Kyari
Abuja - Wani bidiyon da muka samo daga majiya ya nuna lokacin da kotu ke shirye-shiryen zama a yau Litinin a ci gaba da shari'ar Abba Kyari da sauran jami'an da ake zargi da harkallar kwaya.
Abba Kyari da mutum daya daga cikin abokan harkallar tasa sun nemi a ba da belinsu, lamarin da kotun bata amince dashi ba
A zaman kotun ne rahoton jaridar Vanguard ya ce, NDLEA ta kalubalanci batun belin, inda ta bayyana dalilinta na hakan ta bakin lauyan hukumar cewa, watakila Abba Kyari ya tsere bayan ba da belinsa.
Hukumar, a cikin wata takardar bukata mai sakin layi 21 da ta gabatar a gaban kotun, ta dage cewa Kyari na iya tserewa zuwa wata kasa, sannan ya daina halartar zaman kotu, don haka ta nemi a ci gaba da tsare shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A sassauta masa
Sai dai Kyari, a cikin takardar neman belinsa da Mista Mahmud Magaji, SAN ya gabatar, ya roki kotu da ta ba da belinsa bisa sharuddan sassauci.
Hukumar ta NDLEA ta dai nace ta bukaci kotun da ta ki bayar da belin Kyari da tawagarsa, maimakon haka ta nemi a hanzarta sauraron karar.
Bayan sauraran batutuwa daga lauyoyin Kyari da na bangaren NDLEA, alkali ya yi bayani, inda yace za a duba yiwuwar ba da belin a nan gaba.
Daga nan ya dage ci gaba da zama har zuwa ranar 28 ga watan Maris domin yanke hukunci kan bukatar belin da DCP Abba Kyari da wasu jami’an ‘yan sanda 4 suka shigar a zarginsu da ake da harkallar miyagun kwayoyi, TVC News ta rahoto.
Hukumar NDLEA ta gano wasu Biliyoyin kudi kwance a cikin asusun Abba Kyari da yaronsa
A wani labarin, sababbin bayanai su na fitowa a game da tsohon shugaban rundunar ‘yan sanda ta IRT, DCP Abba Kyari da kuma mataimakinsa, ACP Sunday Ubua.
Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa ana zargin wadannan jami’an ‘yan sanda biyu sun karbi Naira biliyan 4.2 lokacin da suke aiki kafin a ruguza tawagarsu.
Wannan yana cikin rahoton da NDLEA ta aikawa Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami.
Asali: Legit.ng